An watsa wa budurwa tafasasshen man gyaɗa a fuska a Zariya

0
197
An watsa wa budurwa tafasasshen man gyaɗa a fuska a Zariya

An watsa wa budurwa tafasasshen man gyaɗa a fuska a Zariya

Daga Idris Umar, Zariya

Wani abin tausayi da ban al’ajabi da ya faru birnin Zariyan jihar Kaduna, inda aka wayi gari da mummunan labarin yadda aka watsa wa wata budurwa tafasasshen man gyaɗa a fuska.

Ita wannan budurwa mai suna Husaina, wadda ke unguwar layin Tanimu Ƙaya, Hayin Dogo, Samaru, a cikin garin Zariya.

Murhun da Husaina ke soya awara

Yadda abin ya faru shi ne, Husaina tana gaban sana’arta ta suyar Awara, wani yaro mai suna Suleiman Abubakar ya zo ya ja ta da cacar baki har ta kai ga zagin mahaifiyarta, ita kuma da ta ji zafi ta rama. Bayan ta rama ne, sai wannan matashi ya sanya ƙafa ya harba mata tafasasshen man da ke kan wutar da take soya Awaran a wannan lokacin.

Nafisa Ibrahim yayar Husaina Ibrahim wacce aka ƙona.

Hakan ya sa nan take fuskarta ta ƙone gaba ɗaya haɗe da wasu sassa na jikinta. Inda nan take kamanninta suka canza kamar ba ita ba.

Ibrahim Ibrahim, wanda ya fara yaɗa lamarin a social media, mazaunin garin samaru

Bayan faruwar lamarin, jama’a suka yi iya bakin ƙoƙarinsu suka damƙe matashin, inda suka miƙa shi ga hukumar tsaro na farin kaya don gudanar da bicike.

Wakilin Neptune Hausa, Idris Umar tare da mai unguwa malam Ibrahim Hasan ( kakale)

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama matar da ta kwara wa mijinta tafasasshen man gyaɗa ta kwaɗa masa guduma ta gudu

Wakilinmu ya ziyarci gidan su Husaina don jin haƙiƙanin abin da ya faru, da kuma ganewa idonsa yadda jikin nata ya ke.

Husaina babu wani kulawa da take samu ta ɓangaren shan ingantattun magunguna don ta samu lafiya mai inganci.

Aliyu Ibrahim mazaunin unguwar da lamarin ya faru tare da wakilin Neptune Prime Hausa

Wakilinmu ya tambayi wasu daga cikin ‘yan’uwanta akan me ya sa aka barta a gida duk da irin halin da take ciki na irin wannan jinya mai buƙatar kulawa ta musamman?

Sai wata daga cikin danginta ta ce, “Wallahi ba wata hanya da za a kaita Asibiti, domin yanzu haka mahaifinmu ma shi ma ba shi da ƙoshin lafiya, ita ce kaɗai take kula da gidan namu, kuma ga wannan bala’in ya faɗo mata sai dai in akwai wanda zai taimaka mana don Allah to” inji ta.

Gidan iyayen Husaina

Husaina dai ‘yar talakawa ce, hasalima da ‘yar wannan sana’arta ta, ta Awara take ciyar da gidan nasu, ga shi yanzu kuma ita ma tana kwance. Hatta kuɗin da za a kai ta Asibiti ma babu, ballantana na abinci. Husaina dai na buƙatar taimako sosai daga al’umma.

Jama’a dai sun zura ido, suna jira su ga wane irin hukunci hukuma za ta yanke wa wannan yaro.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here