An tura matashin da ake zargi da cin mutumci matar Buhari gidan yari

0
315

A ranar talata 29 ga watan Nuwamba ne aka gabatar da Aminu Muhammad matashi kuma ɗalibin jami’a da ake zargi da cin mutuncin matar Shugaban ƙasa Aisha Buhari a gaban kotu kuma tuni aka tisa ƙeyarsa zuwa gidan yari.

Lauyan ɗalibin CK Agu ya tabbatar da cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban kotu da ke Abuja, kuma Aminu bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.

Lauyan wanda ake zargin ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba suka nemi a bada belin Aminu amma hakan bai yu ba. Ya ce a zaman kotun ya sanar da Alƙali cewa sun buƙaci ‘yan sanda su ba da belin Aminu amma suka ƙi.

”Akan haka ne muka buƙaci kotun ta bada shi beli bisa dalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba.

“Yanzu haka kotun ta umurci rundunar ‘yan sanda ta gabatar da buƙatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren buƙatar yau ko gobe,” in ji lauyan Aminu.

Jami’an tsaro sun kama Aminu ne akan rubutun ɓatanci da ake zarginsa da yi akan matar shugaban kasa A’isha Buhari, a shafinsa na tweeter, lamarin da ya ɗauki hankulan masu bibiyar kafafen sada zumunta na zamani inda suka yi ta tattauna zancen.

A baya bayan nan dai ƙungiyar ɗaliban Najeriya ta bukaci mahukunta da su saki ɗalibin cikin awa arba’in da takwas.

Leave a Reply