Daga Ibraheem El-Tafseer
Harry Maguire ya ce Erik ten Hag ya karɓe muƙamin kyaftin ɗin Manchester United daga wajensa.
Ole Gunnar Solskjaer ne ya naɗa Maguire a Janairun 2020, wata biyar tsakani da United ta sayo mai tsaron bayan daga Leicester City kan fam miliyan 80.
Mai tsaron bayan tawagar Ingila ya ce bai ji daɗi kan wannan hukuncin ba, amma zai ci gaba da bayar da gudumuwa kamar yadda ya saba a United.
Mai shekara 30, wanda ya yi wasa takwas a kakar Premier League ta 2022/23, ana alaƙanta shi da zai koma West Ham da taka leda.
Maguire ya buga wa United wasa karawa 31 daga 62 da ƙungiyar ta yi a kakar da ta wuce, inda Bruno Fernandes ke ɗaura ƙyallen kyaftin idan Maguire bai yi wasa ba.
KU KUMA KARANTA: An dakatar da ‘yar tseren Najeriya Nwokocha daga wasanni kan amfani da haramtattun ƙwayoyi
Maguire yana da yarjejeniya tare da ƙungiyar Old Trafford da za ta ƙare a ƙarshen kakar 2025.