An tsinci gawar yaro ɗan wata 16 a Bauchi, an cire wasu sassan jikinsa

0
418

A makon da ya gabata ne, aka tsinci gawar wani yaro ɗan 16, mai suna Muhammad Zainul Abidin da aka bayyana ɓacewarsa tare da cire wasu sassan na jikinsa.

Rahotanni sun ce yaron an bayyana ɓacewarsa ne a lokacin da mahaifiyarsa take rubuta jarabawa a ‘Green Heritage College of Education’ dake Games Village, Bauchi.

Mahaifiyar yaron ce ta ba da labarin yadda lamarin ya faru a wata kafar yaɗa labarai da ake ƙira ‘Labari daga Bauchi.’ Mahaifiyar yaron, Saudatu Abdullahi, ta ce an tsinci gawar ɗan nata bayan an kashe shi, har ya fara ruɓewa, kuma an cire masa Ido, Hanci da Baki.

A cewarta, an tsinci gawar yaron ne a cikin hanyar ruwa (kwalbati) dake cikin makarantar, bayan an shafe kwanaki takwas ana nemansa.

Ta ce tana karatun NCE a Games Village a Bauchi, inda a ranar da lamarin ya faru, wato ranar 19 ga watan Agusta, ta tafi makaranta tare da Abidin kamar yadda ta saba, sai ya fice daga ajin, a yayin da ta ke tsaka da rubuta jarabawa.

A cewar ta, ta saba idan Abidin ya gama yawonsa zai dawo ajin, amma a wannan lokacin shiru bai dawo ba, inda ta bazama nemansa ciki da waje, amma ba ta same shi ba.

“Can na hango takalmansa a kan wani windon wani aji, sai na ɗauka yana cikin ajin. Na yi sauri zuwa can, amma ban ganshi ba. Sai na dawo aji na shaida wa Malaminmu halin da ake ciki.

“Yan ajin mu suka bazama nema kusan ko’ina, amma ba a gan shi ba. Na je na shaidawa, ‘Student Affairs’ shi kuma ya sanarwa ‘yan sanda. Haka a kai ta neman har sai ranar Lahadi aka gano gawarsa ta kumbura kuma duk an cire masa wasu sassan jikin sa,” in ji uwar yaron da take ta sharara kuka yayin da take ba da labarin.

Da ya ke bayani wajen ziyarar ta’aziya da ya kai ga mahaifan yaron, gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Bala Mohammed ya ba da umarnin a rufe makarantar nan take, har sai an kammala bincike.

Leave a Reply