An tsinci gawar wani ƙaramin yaro a ƙarƙashin gada

0
63
An tsinci gawar wani ƙaramin yaro a ƙarƙashin gada

An tsinci gawar wani ƙaramin yaro a ƙarƙashin gada

An tsinci gawar wani yaro ɗan kimanin shekaru uku da haihuwa a ƙarƙashin gadar Oyun da hanyar zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Ilori a Jihar Kwara.

An tsinci gawar jaririn ne bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi ranar Alhamis.

Kwamishinar Muhalli ta jihar, Nafisat Musa Buge, ta tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin.

Ta ƙara da cewa, “gawar ba za ta fi shekara uku da haihuwa ba. Kuma a yadda muka gan ta, da alama ruwan ambaliya ne ya kawo ta ƙarƙashin gadar.

KU KUMA KARANTA: Yan bindiga suna ciyar da karnukansu da naman gawar mutane a Sakkwato — Malami

“Na umarci ma’aikatan ma’aikatar cewa su jira, sai da aka jira tsawon awa 48 bayan tsintar gawar kafin a binne ta.”

Ta ce dalili shi ne, “Kwanaki mun binne gawar wata mata, amma washegari iyalanta suka zo cewa suna neman a tono gawar.”

Kwamishinar ta buƙaci iyaye su riƙa lura tare da sanin inda ’ya’yansu suke, musamman idan ana ruwan sama.

Leave a Reply