Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar ta-ɓaci har zuwa faɗuwar rana don kaucewa taɓarɓarewar doka da oda, biyo bayan tattara sakamakon zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Litinin.
KU KUMA KARANTA: Yadda Abba Kabir Yusuf na NNPP ya lashe zaɓen Kano
Ya ce an yanke shawarar ne don hana ’yan daba su haifar da hargitsi a halin da ake ciki.
Kwamishinan ya yi kira ga jama’ar jihar da su kasance a cikin gida domin jami’an tsaro ba za su ƙyale kowa ko wata ƙungiyar da ke da niyyar haddasa fitina ba.
[…] KU KUMA KARANTA: An sanya dokar hana fita a Kano […]