Connect with us

Boko Haram

An sake ceto ƴan matan Chibok biyu a Jihar Borno

Published

on

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa ta ƙara ceto ƴan matan Chibok guda biyu a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. Babban kwamandan Operation Hadin Kai Manjo Janar Christopher Musa ne ya tabbatar da hakan inda ya ce irin matsin lambar da ƴan Boko Haram ɗin ke fuskanta ne ke sawa suna guduwa suna barin ƴan matan Chibok ɗin.

Manjo Janar Musa ya shaida wa BBC cewa ɗaya daga cikin matan da aka ceto an same ta ne a ranar 29 ga watan Satumba inda aka same ta da yara huɗu.

Yana Pogu, ita ce ta 19 a jerin ƴan matan na Chibok da aka yi garkuwa su.

Ya ce akwai maza biyu da kuma ƴan biyu mata da ta haifa inda ya ce ƴan biyun jarirai ne sabuwar haihuwa.

Ya bayyana cewa dakarun Birged na 21 ne suka gano ta a samamen da suka kai a yankin na ƙauyen na Mairari da ke Ƙaramar Hukumar Bama.

Sa’annan a a ranar 2 ga watan Oktoba, an gano Rejoice Sanki wadda sunanta ne na 70 a jerin yan matan na Chibok da aka yi garkuwa da su.

Ita kuma an gano ta ne yankin Kawuri da ke Ƙaramar Hukumar Konduga tare da ƴayanta biyu.

Kwamandan ya tabbatar da cewa a bana 2022 kawai, an samu nasarar ceto ƴan matan Chibok 11.

Tun a 2014 ne dai ƴan Boko Haram suka sace ƴan mata a makarantar gwamnati ta mata da ke Chibok inda suka kwashe mata 276.

Sai dai tun daga lokacin zuwa yanzu sama da mata 170 suka koma ga iyalansu.

Boko Haram

Boko Haram sun kashe manoma 15 a jihar Borno

Published

on

Wasu da ake zargin ‘yan ƙungiyar Boko Haram ne sun kashe aƙalla mutane 15 a hare-haren da suka kai kan wasu ƙauyuka biyu a ƙaramar hukumar Jere ta jihar Borno.

Kamar yadda rahoton Daily Trust ta ruwaito, ‘yan ta’addan sun kai farmaki ƙauyen Ƙofa ne da tsakar dare inda suka fara harbe-harbe ba da daɗewa ba, wanda har zuwa safiyar Juma’a.

An tattaro cewa maharan sun kuma kai hari a ƙauyukan Molai Kura da Molai Gana inda suka yi ta yanka mutane da ba a tantance adadinsu ba.

KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan Boko Haram suka yiwa masunta 29 kisan gilla, suka jikkata 9 a Gamborun Ngala

Lamarin dai ya sa mazauna yankin da dama sun ƙauracewa gidajensu zuwa wani daji da ke kusa.

Wani jigo a ƙungiyar ’yan banga, Bukar Ali-Musty, ya shaida wa jaridar cewa manoman na aikin gonakinsu ne a kusa da Molai, da ke wajen birnin Maiduguri, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, inda ‘yan tada ƙayar bayan suka kai musu hari suka sare kawunansu.

“Aƙalla gawarwaki 15 ne aka kwashe a safiyar yau, an kai hare-haren ne jiya (Alhamis).

“An sare kan manoma bakwai a lokacin da suke aikin gonakinsu, sannan maharan sun kuma yanka wuya ga wasu fararen hula takwas da ba su da illa a gidajensu,” in ji shi.

Wani memba a ƙungiyar ‘civilian JTF’ da ke cikin tawagar da aka kwashe, ya nuna damuwarsa kan hare-haren, yana mai cewa dole ne duk masu ruwa da tsaki su farka don ganin ba a ci gaba da faruwa ba.

“Abin takaici ne ci gaba idan aka yi la’akari da ci gaban da muka samu a cikin watanni ba tare da an kai wa al’umma hari ba.

“Ina can da safe. Ba zan iya tunanin ganin an yanka ’yan uwana kamar rago ba.

Dukkanin gawarwakin da muka ƙwato an same su ne a cikin kwance cikin jini, kuma ina ganin dukkanmu muna buƙatar mu tashi tsaye domin tunkarar wannan maƙiyin zaman lafiya,” inji majiyar.

Continue Reading

Boko Haram

ISWAP ta kashe mutane uku da jikkata sojoji takwas a Borno

Published

on

Aƙalla ‘yan gudun hijira guda uku ne aka kashe tare kuma da jikkata wasu 13 ciki har da sojoji guda takwas a wasu mabambantan hare-hare da ƙungiyar ISWAP ta kai ƙaramar hukumar Damboa na jihar Borno.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne lokacin da ‘yan gudun hijira guda huɗu da ke zama a sansanin Lowcost a Damboa suka fita domin neman itacen hura wuta lokacin da mayaƙan suka buɗe musu wuta, inda suka kashe uku nan take yayin da sauran mutane kuma suka tsere da raunuka.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun da farko ISWAP ɗin sun jikkata wasu sojoji da kuma fararen hula yayin wani hari da suka kai yankin Talala a ranar Talata duk a Damboa.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa sojoji sun kashe mayaƙan na ISWAP da dama a wani hari da suka kai musu.
Majiyar ta ce wani jrgin sama na sojoji ya je Damboa a jiya Alhamis, inda ta ɗebo sojoji da suka jikkata zuwa Maiduguri domin yi musu magani.

Continue Reading

Boko Haram

Yadda ‘yan Boko Haram suka yiwa masunta 29 kisan gilla, suka jikkata 9 a Gamborun Ngala

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da kashe masunta 29 da ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi a jihar.

Harin wanda ya auku a ƙauyen Mukdolo da ke yankin Gamborun Ngala a jihar ya kuma yi sanadin jikkata wasu masunta guda tara.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Sani Kamilu, wanda ya tabbatar da hakan, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba 8 ga watan Maris, 2023.

A baya dai an ruwaito cewa, ‘yan ta’addan da dama da ke kan babura sun abka cikin filin suna harbe-harbe ba da dadewa ba, yayin da suka kewaye sauran mutane 29 da aka kashe da bindiga bayan da mutane tara suka tsere da raunuka.

KU KUMA KARANTA: Boko haram sun kai hari ƙauyen Borno, sun ƙona runbunan abinci da gidaje

Wata majiya ta shaida wa kafar yada labarai ta yanar gizo, Zagazola Makama, cewa maharan sun yi amfani da gidajen kamun kifi wajen nade masuntan, inda suka azabtar da su sannan suka buɗe musu wuta.

“Sun ce su kwanta. Bayan haka, sun yi amfani da ragarsu na kamun kifi suka naɗe su kafin su fara azabtar da su. Bayan sun suma ne sai suka bude musu wuta, inda nan take suka kashe su,” inji majiyar.

Daga baya an tsinto gawarwakin manoman a wani samame da sojojin da suka samu labarin daga waɗanda harin ya rutsa da su suka tsere daga inda aka kai harin.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like