An kuɓutar da yaran da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna

0
35
An kuɓutar da yaran da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna

An kuɓutar da yaran da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna

Daga Idris Umar, Zariya

An samu nasarar kuɓutar da yaran da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kutsa har cikin gida suka ɗauke yaran huɗu, uku mata, ɗaya namiji ɗan ƙasa da shekara biyu.

Manema Labarai sun yi hira da Iyayen Yaran cikin kuka suke nuna tashin hankali da suka shiga, an sace yaran ne daidai lokacin da mahaifiyar su take jinyar jariran da ta haifa tagwaye a asibiti, yayin da mahaifin su ya tafi gona.

An dai sace Yaran ne a Unguwar Keke, dake ƙaramar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Masu garkuwar sun fara da buƙatar Nera Miliyan 300 a matsayin kuɗin Fansar daga bisani suka rage zuwa Miliyan 25.

KU KUMA KARANTA: Da ni ake haɗa baki, ake garkuwa da mutane a jihar Katsina – Hakimin Runka (Bidiyo)

Hukumomi sun tabbatar da kuɓutar da su cikin koshin lafiya, bayan da aka ga Iyayen yaran da babban mai baiwa Shugaban ƙasa shawara a fannin tsaron ƙasa, Nuhu Ribado da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.

Zuwa yanzu babu cikakken rahoton kan yadda aka kuɓutar da su.

Leave a Reply