An kashe mahauci har lahira a Sakkwato saboda zargin ɓatanci ga Manzon Allah (SAW)

1
260

An kashe wani mahauci, Usman Buds, ma’aikacin mayankar dabbobi na Sakkwato, a jiya, bisa zargin yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

‘Yan uwansa mahauta ne suka kashe wani Bafulatanin Rugar da ke ƙauyen Gulmare a ƙaramar hukumar Gwandu a jihar Kebbi, bayan da wasu mahauta suka kashe shi, bayan sun yi zargin cewa ya yi kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad da zargin ƙin tuba lokacin da abokan aikinsa suka nemi ya yi hakan.

A cewar wani ganau, wanda ya zanta da wakilinmu da ya nemi a sakaya sunansa, Usman Buda a nasa jawabin ya ce ya yi daidai da maganar da Sheikh Abdul Azeez na jihar Bauchi ya yi, inda ya ce bai nemi taimako daga wani mutum ba, ciki har da Annabi mai daraja a Musulunci, sai Allah Maɗaukaki.

KU KUMA KARANTA: Yadda aka kashe mijina Musulmi, mahaddacin AlKur’ani, kan zargin yi wa Annabi ɓatanci’

Ya ce a lokacin da aka nemi Usman ya duba maganarsa ya tuba ya ce ya tsaya kan maganarsa kuma abin da Shehin Malamin ya ce daidai ne yana goyon bayan maganar ɗari bisa ɗari kuma hakan ya tunzura al’ummar Musulmin da ke kusa da shi yayin da aka kashe shi ya mutu har lahira.

Usman Buda ya zauna a unguwar Gidan Igwe tare da iyalansa a cikin babban birnin Sokoto lokacin rasuwarsa.

Kisan Usman Buda ya zo ne kawai shekara guda, lokacin da aka kashe wata yarinya, mai suna Deborah Samuel bisa zargin yin ɓatanci ga Annabi.

Da aka tuntuɓi muƙaddashin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Rufa’i Ahamed, ba a same shi ba duk da ƙiraye-ƙirayen da aka yi masa, saboda ba a samu layinsa ba.

Ƙoƙarin yin magana da shugaban ƙungiyar mahauta ta jihar Sokoto ya ci tura, domin kuwa gidan ma’aikacin ya ɓace jim kaɗan da faruwar lamarin.

1 COMMENT

Leave a Reply