An kama ɓarayin da ke haurawa gidajen mutane suna sata a Yobe

0
90
An kama ɓarayin da ke haurawa gidajen mutane suna sata a Yobe

An kama ɓarayin da ke haurawa gidajen mutane suna sata a Yobe

Daga Ibraheem El-Tafseer

Da safiyar ranar Litinin ne, ana tsaka da ruwan sama, aka kama wasu ɓarayi guda uku, waɗanda suka ƙware wajen haurawa gidajen mutane suna sace musu kayayyaki.

An kama su ne a unguwar Jaji da ke garin Potiskum jihar Yobe, a cikin wani sabon asibiti da ake ginawa, wanda ba a kammala ba.

An same su sun cire dukkan kan famfunan asibitin. Suna tsaka da cire-ciren, dubunsu ta cika aka kama su. Mutanen unguwar ne suka kama su, sannan suka miƙa su ga jami’an tsaron NSCDC da ke Potiskum.

Neptune Prime Hausa ta ziyarci ofishin NSCDC ɗin da ke gundumar Jigawar-Potiskum, kuma ta samu 2IC da ke wajen, Salisu Madu, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce “ba zan yi magana da ‘yan jarida ba, saboda muna kan bincike akan su yanzu haka. Da zarar mun kammala bincike, PPRO ne ke da hurumin magana da ‘yan jarida”

KU KUMA KARANTA: An Kama barayin katin zaɓe 158 a Kano

Wakilinmu ya zanta da ɗaya daga cikin ɓarayin, ga abin da ya ce “suna na Munkaila Isyaka, ni ɗan unguwar Nahuta ne, shekaru na 17.

Da ni makanike ne, daga baya na koma sata. Ba zan iya irga adadin gidajen da na shiga na yi sata ba.

Mu uku muke tafiya, mutum ɗaya zai tsaya a waje, yana gane mana masu wucewa. Mu biyu kuma sai mu shiga cikin gidan.

Abin da muka fi sata shi ne, muna cire duk wani ƙarfe da muka gani a gida, sannan muna zare wayoyin lantarki na cikin gini” inji shi

Ya zuwa haɗa wannan rahoton ɓarayin su uku duka an kama su, suna hanun jami’an tsaron NSCDC ana ci gaba da yi musu bincike, don a gurfanar da su a gaban kotu.