An kama Tukur Mamu, mai shiga tsakani don ceto fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

2
700

Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya, DSS, ta tabbatar da cewa an kama mai kamfanin jaridar Desert Herald, wanda kuma yake shiga tsakani don kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasa da ‘yan bindiga suka sace daga Abuja zuwa Kaduna.

Sanarwar da jami’in yaɗa labarai na hukumar DSS, Peter Afunanya, ya aike wa manema labarai, ta ce ‘yan sandan ƙasa da ƙasa na Ƙasar a Masar su ne suka kama Tukur Mamu a filin jirgin saman a birnin Al-khahira ranar 6 ga watan nan, lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Saudiyya.

Sanarwar ta ce an dawo da shi Najeriya ranar Laraba 7 ga watan Satumba, kuma yana hannun DSS inda ake gudanar da bincike akansa.

Hakan na zuwa ne bayan rundunar soji, da fannin shari’a sun buƙaci abokan hulɗarsu na Ƙasashen waje su dawo da Mamu gida domin amsa tarin tambayoyin da jami’an tsaron Najeriya ke son ya amsa musu, masu alaƙa da batutuwan tsaro da ƙasar ke fama da su.

2 COMMENTS

Leave a Reply