An Gudanar Da Bikin Bude Bodar Jibiya Jihar Katsina

0
283

Daga; Rabo Haladu.

SHUGABAN jami’an hukumar Kwastam ta kasa dake Jihar Katsina, Dalhat Wada Chedi ya jagoranci bikin bude kan iyakar Najeriya da Nijar dake garin Jibia ta jihar Katsina ranar Litinin, 25 ga watan Afrilu, 2022.

Bikin bude bodar dai wanda ya gudana a harabar bodar dake a garin Jibia ya samu halatar masu ruwa da tsaki na sha’anin mulki, harkokin kasuwanci da sarakunan gargajiya na karamar hukumar ta Jibia da jihar Katsina.

Da yake jawabi kafin bude bodar, Kwanturolan Kwastam din ya ja hankalin al’ummar garin na Jibia da su yi anfani da damar da Gwamnatin ta ba su na bude bodar wurin yin biyayya ga umurnin Gwamnati ta hanyar bayar da hadin kai da kuma kwarmata dukkan bata gari.

Daga nan sai ya shawarci dukkan masu sha’awar cigaba ko fara sana’ar shige da fice da sauran kasuwanci tsakanin kasashen biyu da sa tuntubi hukumar kwastam din a yi musu rijista domin gujewa fushin hukuma.

Suma a jawaban su daban-daban, Iwayen kasa na yankin da suka hada da hakiman garin Jibia da Daddare sun godema gwamnatin tarayya bisa jin kukan su da suka yi suka bude bodar sannan kuma suka bayar da tabbacin cigaba da baiwa hukumomin Gwamnati dake yankin dukkan hadin kan da ya wajabta.

Shima shugaban karamar hukumar ta Jibia, Alhaji Bashir Sabi’u Maitan wanda mataimakin sa ya wakilta ya bayar da tabbacin bayar da hadin kai ga Gwamnatin Tarayya da sauran jami’an tsaro domin ganin cewa al’ummar karamar hukumar ta anfana da bude bodar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here