An gano gawarwakin mutum 15 da suka nutse a Kogin Maiduguri

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Aƙalla gawarwakin mutum 15 aka gano a kogin Ngadabul a Maiduguri, babban birnin jihar Borno bayan afkuwar wata ambaliya.

Kodinetan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA a arewa maso gabas, Muhammad Usman, shi ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Maiduguri.

Usman ya ce ana samun ƙaruwar mutane da ke nutsewa cikin kogin sakamakon ambaliya wanda kuma ya shafi al’ummomi da ke kusa da bakin kogin a Maiduguri. Ya buƙaci iyaye da su gargaɗi ‘ya’yansu kan yin ninƙaya a kogin domin kaucewa nutsewa.

Kodinetan na NEMA ya ƙara da cewa hukumar ta samar da kayakin agaji da za ta baiwa waɗanda ambaliyar ta shafa, yayinda kuma take wayar da kan al’umma kan haɗuran ambaliyar ruwa da kuma hanyoyi da za su kare kansu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *