Amurka za ta kammala janye sojojinta daga Nijar ranar Lahadi

0
106
Amurka za ta kammala janye sojojinta daga Nijar ranar Lahadi

 

Amurka za ta kammala janye sojojinta daga Nijar ranar Lahadi

A ranar Lahadi ne Amurka za ta kammala janye dakarunta da kayan aikinta daga sansanin sojin sama da ke Yamai babban birnin ƙasar Nijar a yammacin Afirka, tare da gudanar da bikin janyewar.

Mataki na gaba a ajandar Amurka shi ne ficewarta daga wani sansanin jiragen yaƙi marasa matuƙi na Nijar, wanda aka shirya kammala shi a watan Agusta.

Ficewar dai ya yi daidai da wa’adin ranar 15 ga watan Satumba da hukumomin Amurka da na Nijar suka amince da shi, bayan da sabbin shugabannin sojojin Nijar suka umarci sojojin Amurka da su fice bayan juyin mulkin da aka yi a Yamai a bara.

KU KUMA KARANTA:Sojojin Amurka za su kammala ficewa daga Nijar 15 ga Satumba

Babban hafsan sojin saman Amurka, Manjo Janar Kenneth Ekman, ya na Nijar domin daidaita hanyoyin fita, ya shaidawa manema labarai ta hoton bidiyo cewa za a mayar da yawancin sojojin Amurka da ke Nijar zuwa ƙasashen Turai. Sai dai ya ce an mayar da ƙananan tawagogin sojojin Amurka zuwa wasu ƙasashen yammacin Afirka.

Yayin da Amurka ta janye wasu muhimman kayan aiki daga sansanonin a Nijar, ba ta lalata kayan aiki da kayayyakin da za a bari a baya ba. Da yake nuna fara mai kyau nan gaba, Ekman ya ce, “Manufarmu a cikin aiwatar da hukuncin shi ne, a bar abubuwa cikin yanayi mai kyau gwargwadon iko. Ya ƙara cewa “Idan muka fita muka bar ta cikin rugujewa, ko kuma muka fita ta rashin mutunci, ko kuma idan muka lalata abubuwa kamar yadda muka tafi, za mu hana zaɓin da ƙasashen biyu ke buƙata na gaba. Kuma har yanzu manufofinmu na tsaro suna cikin ruɗani.”

Janjewar musamman daga sansanin jirage marasa matuƙi wani rauni ne ga Amurka da ayyukanta na yaƙi da ta’addanci a yankin Sahel, babban yankin Afirka, inda masu tada ƙayar baya, masu alaƙa da al-Qaida da ƙungiyoyin IS ke gudanar da ayyukansu.

Ekman, wanda shi ne daraktan dabarun yaƙi na rundunar sojojin Amurka a Afirka, ya ce sauran ƙasashen Afirka da ke cikin damuwa game da barazanar ‘yan tada ƙayar baya da ke yankin Sahel, sun tunkari Amurka kan yadda za su haɗa kai da sojojin Amurka domin yaƙar ‘yan ta’adda. “Nijar ta taimaka mana matuƙa a matsayinmu na wuri saboda tana cikin Sahel kuma tana kusa da wuraren da barazanar ta fi ta’azzara,” in ji Ekman. Yanzu ƙalubalen zai fi wahala inji shi, domin shiga yankin sai an samu daga wajen Nijar.

Leave a Reply