Amfanin rumbu wurin ajiye kayan aikin gona

0
181

Rumbu, abin amfani ne na gargajiya da ake adana kayan amfanin gona da manoma suka noma a cikinsa a ƙasar Hausa.

Ana zuba dukkan nau’ukan kayan amfani da ake son adanawa bayan an girbe su daga gona. Ana zuba kayayyaki irin su Hatsi, Wake, Gyaɗa, da sauransu kuma a lokaci guda.

KU KUMA KARANTA: Abubuwan da ba ku ji ba game da ƙasar Mozambik (Hotuna)

Ana amfani da Kara da kuma ciyawar Gamba wajen yin sa. Sannan kuma bayan wannan akwai rumbun ƙasa. Duk dai aiki iri ɗaya suke yi. Kamar yadda ake da ɗakin kara da kuma na ƙasa; Wato ɗakin kago.

An yi amfani da Rumbu na tsawon lokaci kuma an tabbatar da cewa, ya na da tasiri don adana abinci.

Leave a Reply