Ambaliyar ruwa a Zariya ya shafe wani maƙabarta

0
67
Ambaliyar ruwa a Zariya ya shafe wani maƙabarta

Ambaliyar ruwa a Zariya ya shafe wani maƙabarta

Daga Idris Umar, Zariya

Mazauna unguwar Chikaji da ke ƙaramar Hukumar Sabon gari a jihar Kaduna, sun yi ƙira ga gwamnatin jihar da ta kai musu agaji, biyo bayan yadda ambaliyar ruwa ya shafe maƙabartar Hayin-Ojo wanda yanzu haka da yawa ana ganin likkafanin mamata a filin Allah.

Wannan ƙiran ya biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da ya jawo ambaliyar ruwan ne da yayi sanadin rushewar gidaje masu dama.

Ambaliyar ya fi shafar yankin da ke kusa da magudanar ruwa daga Yan-awaki kusa da zagayen Kano zuwa Chikaji har zuwa Shika dam dake Sabon Gari.

Dagacin garin Chikaji, Alhaji Auwal Sani-Danbaba, ya shaida wa manema labarai cewa ambaliyar ta lalata gidaje sama da 200.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa a Arewa ta kashe mutum 49, ta raba 41,344 da muhalli – NEMA

Kazalika, ta shafe wani ɓangare na Makarantar Firamare ta LEA da kuma wani ɓangare na Makabartar Hayin Ojo.

Amma ba a samu rahoton asarar rayuka ba zuwa haɗa wannan rahoton.

Ɗanbaba, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan rashin samun ɗauki ko agaji daga gwamnati ko wata hukuma.

Ya jaddada buƙatar gaggawar ɗaukar mataki daga hukumomin da ke kula da lamarin da ya shafi Iftila’in ambaliyar ruwa a jihar.

Suleiman Liman, babban limamin Masallacin Chikaji, ya bayyana cewar sun kira wani taron gaggawa na masu hannu da shuni domin magance matsalar da ta shagi maƙabartar da kuma taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa.

Wani mutum da ambaliyar ta shafa ya ce yayin da suke ƙoƙarin kwashe ruwan da ya shiga gidansu, wani ɓangare na ginin gidan ya rushe.

Ya ce babbar damuwarsu shi ne yadda za su kare ‘ya’yansu daga baraguzan ginin.

Ya roƙi tallafi da gaggawar ɗaukar mataki daga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Wakilinmu ya gano cewa yawancin waɗanda ambaliyar ya shafa suna zaune ne tare da ‘yan uwansu, yayin da wasu matan aure suka koma gidajen iyayensu kafin su sami wani matsugunin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here