Gwamnatin Nijar ta sa hannu kan kundin tattara bayanan ‘yan ta’adda

0
102
Gwamnatin Nijar ta sa hannu kan kundin tattara bayanan 'yan ta'adda

Gwamnatin Nijar ta sa hannu kan kundin tattara bayanan ‘yan ta’adda

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sa hannu kan wata doka ta kundin tattara bayanan ‘yan ta’adda, wadda za ta taimaka wajen ƙarfafa yaƙi da ta’addaci da ayyukan da ke barazana ga tsaron ƙasar.

Dokar wadda shugaban ƙasar Birgediya Janar Abdurahamane Tiani ya sanya wa hannu a ranar 27 ga watan Agustan 2024 ta tanadi hukunci mai tsauri ga duk wanda aka samu da laifi.

Hukumomin Nijar dai sun ƙirƙiro kundin ne don rajistar bayanan duk wani mutum ko wata ƙungiya da ke da hannu a ayyukan ta’addanci.

Daga yanzu, za a riƙa yin rajistar duk wani da ke da alaƙa da ayyukan ta’addanci a cikin kundin na ƙasa, sannan za a karɓe shaidar mutum ta ɗan kasa na wani ɗan lokaci ko na dindindin tare da sauran wasu hukunce-hukunce masu tsauri, kana kwamitin tattara bayanai na ƙasa ne zai ringa sa ido a kan aiki da dokar da kuma kudin.

KU KUMA KARANTA: Nijar ta ɓullo da wasu matakan inganta rayuwar marasa lafiya kyauta

Duk wani mutum ko ƙungiya ko ma’aikata da bayanansu suka shiga cikin kundin, za a hana su yin balaguro a cikin ƙasar har ma da ƙasashen waje tare da sanya takunkumi a hada-hadar kasuwanci da kuma rufe ƙadarorinsu.

Kazalika, dokar ta tanadi karɓe takardar shaidar ɗan ƙasa sannan idan aka yanke wa mutum hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar ko fiye da haka za a kwace shaidarsa ta ɗan kasa na dindindin.

Wannan sabon tsarin dai na zama wani gagarumin mataki a ƙoƙarin da gwamnatin Nijar ke yi na kawar da barazanar tsaro tare da samar da zaman lafiya a ƙasar wadda ke yankin Yammancin Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here