Ambaliyar ruwa a Jigawa tayi sanadiyar mutuwar mutane 16 tare lalata gidaje da dama
Daga Shafaatu Dauda, Kano
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA), ta tabbatar da mutuwar mutane 16 tare da lalata gidaje 3,936 sakamakon ambaliyar ruwa.
Ya kuma ce ambaliya ta kuma mamaye gidaje 2,744 na gonaki biyo bayan mamakon ruwan sama tun da aka fara daminar shekarar 2024
Sakataren zartarwa na hukumar, Dakta Haruna Mariga, wanda ya bayyana hakan a Dutse ranar laraba, ya ce bala’in ya shafi ƙananan hukumomi 10 na jihar.
KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa ta lalata ƙananan hukumomi 3 a Kano – SEMA
Mairiga ya ce mutanen sun mutu ne sakamakon rugujewar gini, nutsewa da kwale-kwale.
Ya ce bala’in ya yi sanadin mutuwar mutane 16 tare da mutane 3,936 da suka rasa matsugunansu yayin da hekta 2,744 na gonaki suka nutse,” in ji shi, ya ƙara da cewa lamarin na iya ƙara kamari saboda yawan ruwan sama da ake sa ran zai yi.
Mairiga ya ce hukumar ta samar da matsuguni na wucin gadi tare da raba kayan agaji ga ‘yan gudun hijirar domin rage musu raɗaɗi.