Daga; JABIRU A HASSSN, Dutse.
SHUGABAN Kungiyar manoma ta kasa (AFAN), reshen jihar Jigawa Alhaji Idris Yau Mai Unguwa, ya taya al’ummar musulmi murnar shigowa wata mai alfarma na Ramadan.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Idris Yau mai Unguwa ya bayyana cewa yana fata al’ummar musulmi a duk inda suke, za su yi amfani da darussan da suka koya wajen kyautata zamantakewa su tsakanin su da sauran al’umma, tare da fatan samun rabauta daga dukkanin alherin dake cikin wannan wata.
Haka Kuma Mai Unguwa ya bukaci al’ummar musulmi da su kara yin addu’oi na samun dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Jigawa da Najeriya da Kuma duniyar musulmi a duk inda suke, tare da yin fatan alheri ga Gwamnan Jihar ta Jigawa Muhammad Badaru Abubakar da Gwamnatin sa da Kuma daukacin manoman Jihar.
A karshe, Idris Yau mai Unguwa, ya jaddada cewa zasu ci gaba da yin shugabanci mai kyau ga manoman Jihar Jigawa ta yadda sana’ar su ta noma za ta ci gaba da kasancewa mai riba rani da damina.