Adawa Da Hassada Kawai Ake Yadawa Kan Takarar Tinubu

0
327

Wasu daga masu goyon bayan takarar shugabancin kasar tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyar APC Mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu, sun ce mahassada ne ke makala masa rashin lafiya don ba su son ya tsaya takara a 2023.

A jiya ne Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa ta neman shugabancin Najeriya, lokacin da ya kai ziyara ga shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

To amma akwai masu ganin jigon ba shi da cikakkar lafiyar da yakamata a ce ya mulki kasar.

Alhaji Ibrahim Masari shi ma kusa ne a jam’iyyar, wanda ya taba zama sakataren walwala na jam`iyar ta APC, kuma daya daga cikin makusantan Bola Tinubu, kuma ya fada wa BBC cewa a ganinsu Tinubu na da cikakkar lafiyar da zai jagoranci Najeriya ba tare da wata matsala ba.

Masari ya buga misali da shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce ” in ba ka manta ba da sanin ka ne ‘yan jarida aka yi ta yawo da makara a na cewa ai matacce ne ya mutu gobe za a kawo gawarshi jibi za a kawo gawarshi.”

“Saboda haka duk wanda ka ji yana cewa wani ba shi da lafiya tsabar hassada ce da jin zafi, mutumin ya tarbe mai gaba ya rasa yadda zai yi da shi, sai ya bata masa suna ko kuma ya karya wa wadanda suke da ra’ayin wannan mutumin guwayu ga nashi tunanin.” A cewar Ibahim Masari.

Ya kara da cewa kowa ya ga yadda Tinubu ya taka da kafarsa har wurin shugaban kasa ba tare da an dora sa a kan kujera ku an rika shi ba.

Saboda haka yace batun rashin lafiya ko lafiya ” ya rage ruwan mai fadi ya je ya ta fadi.”

Baya ga batun lafiyar Bola Ahmed Tinubu, wani abu da ke yawo shine batun cewa shi musulmi ne kuma idan har zai tsaya takara da wahal ya dauki wanda ba musulmi ba a Arewacin Najeriya.

Hakan na nufin akwai yiwuwar in har jam’iyar ta tsayar da shi takara, to kuwa ta yiwu za ta tsayar da musulmi da musulmi takarar shugaba da mataimakinsa a zaben na 2023.

Bugu da kari batun yiwuwar takarar mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da tuni wasu suka fara dasa allunansa ta hadu da cikas, ganin cewa ga ubangidansa a siyasa ya fito.

To amma kan wannan batu na takarar Farfesa Yemi Osinbajo Ibrahim Masari na ganin cewa a wannan gabar yakamata mataimakin shugaban kasar ya gane cewa “mai wuri ya zo mai tabarma ya nade.”

Masu lura da lamuran siyasa suna gani Tinubu zai fuskanci ƙalubale wajen samun tikitin yi wa APC takarar shugaban ƙasa a 2023, musamman ganin yadda shekarunsa suka ja kuma ‘yan kasar na fatan ganin an zabi mai jini a jika.

Sai dai wasu ƴaƴan jam’iyyar na ganin ya kamata a saka masa da wannan takara ko don irin wahalar da ya yi wa APC da Shugaba Muhammadu Buhari a zaɓukan 2015-2019.

Akwai kyakkyawan zaton cewa APC za ta miƙa wa yankin kudu maso yammacin Najeriya takarar shugaban ƙasa a 2023, don haka ake ganin cewa Tinubu wanda uban gidan Osinbanjo ne a siyasance, a wannan karon zai ɓarje guminsa.

Wasu kuma na ƙishin-ƙishin cewa ba lallai ne wasu gwamnonin jam’iyyar ta APC musamman a arewacin ƙasar su goyi bayan Tinubu ba, yayin da wasu ke ganin cewa ya yi kafuwar da ture shi a jam’iyyar sai an shirya.

Leave a Reply