Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
MATAIMAKIYAR Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe, ta bayyana cewa karamar hukuma Kawuru ce na farkon da aka fara gudanar da sabon tsarin shirin aikin gina al’umma wanda Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya gudanarwa.
Hadiza Sabuwa, ta furka hakan ne a lokacin da ta ke jawabi a ziyarar da ta kai karamar hukumar don ganawa da mutanen garin, kana da Ƙaddamar da sabon shirin aikin gina al’umma wato Human Capital Develpment Capacity Building (CABs) wanda zai tallafawa al’umma musamman mata da yara.
Ta kara da cewa wannan wani babban abun alfari ne a gare ta da Gwamnatin Jihar domin tunkarar tsarin taimakawa al’ummar Jihar domin ganin sun samu damar dogaro da kansu musamman a yanzu da tattalin arzikin Kasar ke cikin wani mawuyacin hali.
Ta ce “na yi matukar kasance a nan tare da ku a kauru don na jima ban samu zuwa na kawo muku ziyara ba, kuma abin da baku sani ba shi ne karamar hukumar Kauru ce ta farko da muka fara gudanar da wannan shirin, kuma farin cikina shi ne nima ina cikin wannan shirin da aka fara a nan garin Kauru.’
“Shi wannan shirin na gina al’umma da mu ke yi, Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauke shi da mahimmanci sosai, domin shi ne tushen duk wani abin da muke yi a nan Jihar Kaduna, domin akwai bincike da ake yi duk kasashen duniya da yake nuna cewa idan muka ba da karfa ga gina al’umma, za mu ga wannan kasar ta na ci gaba sosai.”
“A cikin kasashe 189 da aka duba, mu muka zo na 161, wato mun buge kasashe 27, toh wannan abu ya nasa damuwa, don haka muna so muga mun zama na daya ko da biyu amma musan hakan ba zaiyu ba kai tsaye sai mun hada Karfi da karfe ta hanyar hadin kan al’umma, saboda Ilimi, kiwon Lafiya da aikin yi sune ke kawo ci gaba.”
“Don haka duk wani yaro mu yi kokarin muga mun sasu a Makaranta. Abu na biyu shi ne akwai wuraren kiwon Lafiya da aka yi gyare-gyare a duk fadin Jihar, mu rika kokari muna amfani da su saboda idan ba a amfani da su, za mu samu ci gaban da ake bukata ba.”
Mataimakiyar Gwamnan, ta kara da yin kira ga masu Sarautun Gargajiya da sauran al’umma da su rungumi shirin da mahimmanci ta hanyar kara wayar da kan al’umma, kana da yin amfani da wannan damar wajen ganin sun amfana da shirin ta hanyar ci gaba da zama wadanda suka kasancewa na daya kamar yadda suka kasancewa na farko a tsarin shirin.
A karshe, Hadiza Sabuwa Balarabe, ta shawarci al’ummar yankin tare da Jan hankalinsu da su kaucewa yin duk wani abun da zai gurbata musu wannan tsarin da ke da nasaba da bunkasa tattalin arzikin Jihar da Kasar baki daya.