A gabana ‘yan sanda suka kashe makiyaya, bayan Abba Kyari ya nemi in ɗorawa Saraki laifin fashi – Ɗan fashi ga Kotu

3
578

Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da laifin fashi da makami a bankin Offa, Ayoade Akinnibosun a ranar Larabar da ta gabata, ya shaida wa wata babbar kotun jihar Kwara da ke zaune a Ilorin, yadda tsohon kwamandan, Response Team, Abba Kyari, ya azabtar da shi tare da yi masa alkawarin ba shi N
naira 10 da sauran abubuwa, domin ɗorawa tsohon shugaban majalisar dattawa, Dokta Bukola Saraki laifin fashi da makami.

Ya ce baya ga haka, Abbas Kyari ya yi alkawarin ba shi takardar bizar kasar da ya ga dama idan ya goyi bayan matakin da aka ɗauka na zargin Saraki, amma ya ce ya yi watsi da tayin.

‘Yan sanda sun gurfanar da wasu mutane biyar, Ayoade Akinnibosun, Ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, Salaudeen Azeez da Niyi Ogundiran a gaban kotu bisa laifin haɗa baki na fashin banki, mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, kisan gillar ‘yan sanda tara da wasu farar hula da harin ‘yan fashin ya rutsa da su a jihar Kwara.

KU KUMA KARANTA:‘Yan sanda sun kama tsohon soja da ya zama ƙasurgumin dan fashi a Zamfara

A yayin da lamarin ya faru, kimanin mutane 11 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu suka samu munanan raunuka.

A wata shaida da lauyan masu ƙara, Mathias Emeribe (SAN) ya jagoranta, Akinnibosun ya ce an ba shi naira miliyan 10 don yayi ikirarin cewa Bokola Saraki ne ya sasu su yin fashin.

“Shi (Kyari) ya ce in yarda kuma in ce Saraki ne ya ce mu je mu yi fashi,na ce masa ba zan yi haka ba, domin da nayi haka gwara in mutu don abin da ban yi ba, akan na yi ƙarya ga mutumin da ba shi da laifi.

“Ya kuma ce in yi tunani a kan tayin nasa sosai, a nan ne ya umarci jami’an ‘yan sanda guda biyu, Hassan da Mashood da su mayar da ni gidan yari daban da inda wasu suke, su daina azabtar da ni,” inji shi.

Akinnibosun ya ce ba a ba shi damar rubuta wata sanarwa a Ilorin ba sai dai bayan haihuwarsa, har sai da aka kai su Abuja a cikin wata motar bas, inda daga baya aka ajiye shi a wani wuri da ake kira “Abattoir”.

A can, wanda ake zargin, ya ce an kashe wasu makiyaya a gabansa, inda ya ƙara da cewa an azabtar da shi ba tare da tausayi ba, an kuma harbe shi a kafarsa domin ya sanya Saraki cikin badaƙalar.

Akinnibosun ya ƙara da cewa an harbe ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da aikata fashin mai suna Michael Adikwu a gabansa, lamarin da ya sanya shi firgita kuma ya sa ya amince ya sanya Saraki a lokacin da aka gurfanar da shi a gaban manema labarai.

Alkalin kotun mai shari’a Halimat Salman ta ɗage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 13 ga watan Fabrairun 2023.

3 COMMENTS

Leave a Reply