Ana samun ci gaba a ɓangaren tsaro a jihar Kaduna– Sarkin Zazzau

0
327
Ana samun ci gaba a ɓangaren tsaro a jihar Kaduna– Sarkin Zazzau

Ana samun ci gaba a ɓangaren tsaro a jihar Kaduna– Sarkin Zazzau

Daga Idris Umar, Zaria

Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ne ya bayyana hakan a saƙonsa na sallar bana ga mutanen ƙasar Zazzau da Jihar Kaduna baki ɗaya.

A cikin sakon,Sarkin ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a cigaba da kula da tsaro a kowanne yanki, inda ya bukaci mazauna yankunan su kula da duk wani motsi ko shigar baƙi yankunansu, tare da kai rahoton irin wannan motsi ga hukumomi.

KU KUMA KARANTA:Talakawa suna girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi

Hakanan, Sarkin ya yi kira ga iyaye da su sanya ido sosai kan harkokin yara da abokansu domin tabbatar da tsaro. Ya kuma yi godiya ga Gwamna Uba Sani bisa aiwatar da manyan ayyukan ci gaba a fadin jihar, inda ya bayyana cewa wannan yana daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen inganta yanayin tsaro.

A cikin sakon, Sarkin ya kuma yaba da aikin jinƙai da Dr. Tajuddeem Abbas, Iyan Zazzau, ke yi na tallafawa al’umma da kayan abinci, yana mai cewa wannan na daga cikin abubuwan da suka kawo ci gaba a cikin al’umma.

Har ila yau, Sarkin ya gargadi sarakunan gargajiya da su guji duk wani zalunci ko kuma ayyukan da ba su dace ba wajen mu’amala da talakawansu. A ƙarshe, ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin Ramadan, tare da addu’ar Allah ya karɓi azumin su.

Leave a Reply