Mummunan hatsarin mota a Yobe, ya kashe mutane 10, uku sun jikkata

0
91
Mummunan hatsarin mota a Yobe, ya kashe mutane 10, uku sun jikkata

Mummunan hatsarin mota a Yobe, ya kashe mutane 10, uku sun jikkata

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wani mummunan hatsari da ya auku a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a ranar Talata, wanda ya yi sanadin asarar rayuka 10 tare da jikkata wasu mutane uku, kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta tabbatar.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan SP Dungus Abdulkarim, hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na safe a wani shingen bincike na jami’an tsaro a garin Warsala. Wata babbar motar dakon siminti da fasinjoji ta ƙwace, ta yi karo da wata mota, sannan ta faɗa cikin wani rami.

KU KUMA KARANTA:NSCDC a Yobe ta cafke mutane 17 kan aikata laifin sata

“Goma daga cikin fasinjoji 13 da ke cikin tirelar sun mutu nan take, yayin da uku suka samu munanan raunuka,” in ji Abdulkarim. An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin ƙwararru da ke Damaturu domin ba su kulawar gaggawa .

Binciken farko ya nuna cewa direban babbar motar, motar ce ta ƙwace masa, ya rasa yadda zai yi, lamarin da ya yi sanadin hatsarin da ya biyo baya. Wani abin mamaki shi ne wanda ke cikin motar ya tsira da ransa ba tare da ya samu rauni ba, duk da cewa motar ta yi kwatsa-kwatsa.

Zuwa haɗa wannan rahoton, ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin.

Leave a Reply