Cikin kwanaki uku, cutar kwalara ta kashe mutane 60 a Sudan ta kudu

0
37
Cikin kwanaki uku, cutar kwalara ta kashe mutane 60 a Sudan ta kudu

Cikin kwanaki uku, cutar kwalara ta kashe mutane 60 a Sudan ta kudu

Wata barkewar kwalara a Sudan ta Kudu ta hallaka kusan mutane 60 kana ta kwantar da kimanin 1,300 a asibiti a cikin kwanaki uku, a cewar hukumomin lafiya a ranar Asabar.

Ana zargin rashin ruwa mai tsafta ne ya haddasa barkewar kwalara a birnin Kosti dake kudancin kasar bayan da injin bada ruwa na birnin ya daina aiki sakamakon harin da wata kungiyar sojojin sa kai ke yi, a cewar ma’aikatar kiwon lafiya. Kungiyar ta kwashe kimanin shekaru biyu tana fada da sojojin kasar.

KU KUMA KARANTA:Zargin ɓullar cutar Ebola, NCDC ta tsaurara bincike a iyakokin Najeriya

Ma’aikatar ta fada a wata sanarwa cewa cutar ta kashe mutane 58 kana ta yi sanadin kwanciyar wasu 1,293 a asibiti tsakanin ranar Alhamis da Asabar.

Ma’aikatar kiwon lafiyar ta ce ta dauki jerin matakai domin yaki da cutar, ciki har da kaddamar da shirin rigakafin cutar kwalara a cikin birnin.

Cutar ta kashe sama da mutane 600 ta kuma kwantar da sama da dubu 21 tsakanin watan Yuli da Oktoban bara.

Cutar kwalara dake sa yawan zawo tana yaduwa cikin gaggawa, tana kai ga rashin ruwa a jikin dan Adam tana kuma iya yin lahani idan ba a dau mataki nan da nan ba, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO. Tana kuma yaduwa ne a cikin abinci da ruwa da suka gurbace.

Leave a Reply