EFCC a Gwambe, ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a

0
26
EFCC a Gwambe, ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a

EFCC a Gwambe, ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi da su guji almundahana tare da yin amfani da kuɗaɗen jama’a bisa gaskiya da adalci.

Shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede ne, ya bayyana haka yayin wani taro da aka shirya a Jihar Gombe kan ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi.

A cewarsa, samun ‘yancin cin gashin kai ba yana nufin cewa shugabannin ƙananan hukumomi ba za a iya hukunta su ba idan sun aikata ba daidai ba.

“Shugabannin ƙananan hukumomi ba su da kariya a tsarin mulkin ƙasa. Idan aka samu rashin gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a, dole ne a ɗauki mataki,” in ji Olukoyede.

KU KUMA KARANTA:EFCC a Abuja ta kama ‘yan China 4 bisa zargin damfarar Intanet

Ya kuma bayyana cewa EFCC za ta ƙara tura jami’anta zuwa Jihar Gombe domin sanya ido kan yadda ake sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Har ila yau, Olukoyede ya yaba wa hukuncin Kotun Ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi damar samun cikakken iko kan kuɗaɗensu, inda ya ce hakan zai taimaka wajen inganta ayyukan ci gaba.

Sai dai ya nuna damuwa kan yiwuwar wasu su karkatar da kuɗaɗen da aka ware don ayyukan al’umma.Ya yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomi da su bi doka wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a.

Ku tabbatar da gaskiya a dukkanin ayyukanku, ku kuma san dokokin da suka shafi amfani da kuɗaɗen jama’a. Rashin sanin doka ba hujja ba ce,” ya gargaɗe su.

Taron, wanda aka yi wa take da “’Yancin Cin Gashin Kai na Ƙananan Hukumomi: Samar da Ci Gaba Mai Ɗorewa,” ya mayar da hankali ne kan yadda ake iya amfani da kuɗaɗen jama’a ta hanyoyin da za su amfanar da al’umma.

Leave a Reply