‘Yansanda a Abuja sun gano motar da aka sace ta hanyar amfani da na’urar bibiya

0
33
'Yansanda a Abuja sun gano motar da aka sace ta hanyar amfani da na’urar bibiya

‘Yansanda a Abuja sun gano motar da aka sace ta hanyar amfani da na’urar bibiya

Rundunar ‘Yansandan babban birnin tarayya Abuja, ta samu nasarar gano wata Mota da aka sace, ta hanyar amfani da na’urar bibiya ta zamani (Tracker).

Kakakin rundunar a Abuja, SP Josephine Adeh, ce ta sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta aiko wa jaridar GTR Hausa a safiyar yau Lahadi, inda ta ce sun gano Motar ne kirar Lexus GS460, samfurin 2016.

A cewar Josephine, “A kokarin da muke yi na kakkabe ayyukan bata-gari, Jami’anmu sun sami sami nasarar gano Motar da aka sace a kusa da babban titin Kubwa, da misalin karfe Bakwai na ranar Alhamis din da ta gabata.

KU KUMA KARANTA:Hukumar NSCDC ta kama mutane 7 da ake zargi da sace murafan kwalbati

“Kuma dai mun sami nasarar ne ta hanyar amfani da na’urar bibiya ta zamani (Tracker), inda bata-garin suka yadda Motar bayan sun gano muna bibiyar su, wanda tuni Motar na hannunmu inda muke kokarin gano wadanda ake zargi”.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja, CP Olatunji Disu ya shawarci masu ababen hawa da su sanya Na’urar, domin yin kandagarki dama saukaka wa musu aikin gano musu su, idan sun fada hannun masu mugun nufi irin wadannan.

A karshe rundunar ta bukaci al’umma su ci-gaba da sanya idanu akan dukkan wani motsi da basu gamsu da shi ba, domin bada rahoto ta wadannan lambobin waya 08061581938, ko 08032003913, da kuma 08028940883.

Leave a Reply