‘Yansanda a Kano, sun kama amarya bisa zargin sanya guba a abincin bikinta

0
26
'Yansanda a Kano, sun kama amarya bisa zargin sanya guba a abincin bikinta

‘Yansanda a Kano, sun kama amarya bisa zargin sanya guba a abincin bikinta

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Rundunar ‘yansanda ta Jihar Jigawa ta tabbatar da kama wata amarya da ake zargin ta sanya guba a abincin da aka bai wa baki a liyafar bikinta da aka yi a Karamar Hukumar Jahun ta jihar.

wannan mummunan lamari ya sa an kwantar da ango a asibiti a mawuyacin hali, yayin da daya daga cikin baki ya rasa ransa.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na yansandan jihar, Lawal Shi’isu Adam, ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike kan al’amarin.

KU KUMA KARANTA:Allah Ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Slow rasuwa

“Mun samu rahoton cewa amaryar ta sanya guba abincin da aka ba wa baki a liyafar bikinta, wanda hakan ya jawo ango ya shiga mawuyacin hali.

“Za mu yi duk mai yiwuwa don ganin an yi adalci,” inji shi.

A cewar kakakin yansanda, duk baki na liyafar da suka ci abincin da aka sanya wa guba sun warke daga asibiti, banda mutum daya da aka tabbatar da rasuwarsa.

Leave a Reply