Adadin man fetur da ake sha a Najeriya ya ragu – Rahoto

0
79
Adadin man fetur da ake sha a Najeriya ya ragu - Rahoto

Adadin man fetur da ake sha a Najeriya ya ragu – Rahoto

Adadin man fetur da ‘yan Najeriya ke amfani da shi a kowace rana ya ragu tun bayan da Shugaba Bola Tinubu, ya soke tallafin man fetur.

Alkaluman da hukumar kula da albarkatun ruwa da na kasa, sun nuna cewar ana shan lita miliyan 60 a watan Mayun 2024.

Amma a watan Agustan 2024, alkaluman sun sauya zuwa lita miliyan 4.5 a kowace rana.

Wannan ne ya nuna cewar an samu raguwar man da ake sha wanda ya ragu da kashi 92 cikin 100.

Bayanan hukumar sun nuna cewa a cikin jihohi 36 guda 16 ne suka karbi mai daga kamfanin NNPCL wannan wata.

KU KUMA KARANTA: Dalilin da ya sa mu ka sake ƙara farashin man fetur — NNPC

Kazalika, ya nuna cewar duk jihohin da ba su karbi mai daga kamfanin ba sun fuskanci karancinsa da dogayen layuka a gidajen mai.

Bayanai sun nuna cewar Jihar Neja ce ta fi samun mai da yawa, inda aka kai mata mota 21 kimanin lita 900,040 sai Jihar Legas da ta karbi mota 12 sama da lita 700,026, Jihar Kaduna an kai mata mota 12 kimanin lita 400,054.

Sauran jihohin da suka samu adadi mafi yawa sune Oyo inda aka kai mata mota 12 dauke da lita 400,054 sai Kano mai mota tara, Kwara mota shida, Edo mota hudu, sai Babban Birnin Tarayya, Abuja mota hudu.

Tinubu ya cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu 2023, bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.

Shugaban ya ce biyan tallafi ba abu ne mai dorewa ba duk da ‘yan Najeriya sun ki aminta da shi.

Matakin ya sa man fetur kara fara, wanda a yanzu haka ana sayar da shi sama da Naira 1000 a gidan man gwamnati na NNPCL.

Leave a Reply