Gwamna Abba ya ɗauki nauyin kula da marayu 95
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna karamci ta hanyar ɗaukar nauyin kula da rayuwar marayu 95 da ke jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata liyafar cin abinci tare da yaran da suke zaune a gidan marayu na jihar bayan rasa iyayensu.
Liyafar cin abincin na ɗaya daga cikin abubuwan da gwamnan ya shirya domin murnar Ranar ‘Yancin Kai ta 2024 a Kano.
Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa Gwamna Yusuf ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin marayun 95.
“Ina so na sanar da cewa mun ɗauki cikakken nauyin marayu 95 da ke zaune a wannan waje. Za mu kula da karatunsu daga Firamare har zuwa Jami’a.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta karɓo bashi daga Faransa domin aikin ruwan sha
“Za mu kula da lafiyarsu, abinci da kuma duk wasu buƙatunsu na yau da kullum a tsawon wa’adin mulkina,” in ji Gwamnan.
Gwamna Yusuf, ya bayyana cewa za a kula da yaran sosai, tare da tabbatar da cewa sun samu duk wata kulawa da goyon bayan da ya dace yayin da yake kan mulki.
Ya kuma ce gwamnatinsa za ta samar da dama ga yaran domin su cimma burinsu a rayuwa.
Gidan marayun, wanda aka samar da shi shekaru 54 da suka gabata, ya samu wannan karamci ne daga Gwamna Yusuf, wanda ya shafe tsawon lokaci tare da yaran.
“Yanzu kun zama yarana, kuma zan kula da ku kamar ‘ya’yana. Za ku fara jin daɗin rayuwa, Insha Allah,” in ji Gwamnan.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa Gwamnan ya bayar da kayan abinci na miliyoyin Naira domin tallafa wa jin daɗin rayuwar marayun, tsaro da kuma samun wadataccen abinci.