Jami’an tsaro sun kama mutane 15 da ake zargi da safarar makamai ga ‘yan ta’adda

0
140
Jami'an tsaro sun kama mutane 15 da ake zargi da safarar makamai ga 'yan ta’adda

Jami’an tsaro sun kama mutane 15 da ake zargi da safarar makamai ga ‘yan ta’adda

Rundunar Sojojin Najeriya tare da haɗin gwuiwar wasu hukumomin tsaro sun kama mutane 15 da ake zargin suna safarar makamai da kayan aiki ga masu ‘yan ta’adda.

A sakamakon samun bayanan sirri, sojojin sun kai farmaki a wurare daban-daban, inda aka kama waɗannan mutane tare da kwace makamai da alburusai masu yawa. An kashe wani da ake zargin ɗan ta’adda ne yayin wani samame.

A ranar 30 ga Agusta, 2024, an gudanar da wani samame a ƙauyukan Mararaba Donga da Manya a jihar Taraba, inda aka kama mutane biyar da ake zargi tare da kwace makamai da dama, ciki har da bindigogi kirar AK-47, bindigogin da aka ƙera da kuma alburusai da sauran kayan aiki.

Haka zalika, an kama wasu mutum uku da ake zargin suna safarar kayan masarufi ga Boko Haram a jihar Yobe, inda suka shafe sama da shekaru biyu suna aiki tare da taimakon yan banga na yankin..

KU KUMA KARANTA: Matsalar Tsaro: Ministan tsaro, shugabannin sojojin Najeriya za su tare a Sokoto

Abubuwan da aka ƙwace daga hannunsu sun haɗa da motoci, babura, kayan gyaran babura, da kuma magunguna.

Bayan haka, an gudanar da wasu samame a jihar Kaduna inda aka kama wasu mutum huɗu da ake zargi suna safarar makamai da kayan aiki. Sojojin sun ƙwace alburusai, wayoyin hannu, katinan caji, da kuma kuɗi masu yawa.

A jihar Edo, an kashe wani shahararren ɗan fashi yayin wani artabu, kuma a jihar Filato, an kama wasu mutum uku da ake nema ruwa a jallo kan sace-sace tare da makamai a hannunsu.

Leave a Reply