Mutane 29 sun mutu a hatsarin jirgin kwale-kwale a Kongo

0
111
Mutane 29 sun mutu a hatsarin jirgin kwale-kwale a Kongo

Mutane 29 sun mutu a hatsarin jirgin kwale-kwale a Kongo

Adadin waɗanda suka mutu sakamakon hatsarin jirgin kwale-kwalen a yammacin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya ƙaru zuwa aƙalla 29 tare da gano aƙalla mutum 128 da suka tsira da rayukansu, wasu kuma ba a san adadinsu ba, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar a ranar Alhamis.

An kwashe kwanaki ana aikin ceto bayan kwale-kwalen da ke ɗauke da fasinjoji tsakanin 250 zuwa 300 ya kife a daren Lahadin da ta gabata a lokacin da ya afka cikin kututturen bishiya a karkashin ruwa a wani kogi a yankin Kutu.

KU KUMA KARANTA:Hatsarin jirgin ruwa ya laƙume rayukan mutane 9 a Zamfara

“Ɗaukar fasinjoji fiye da kima da tafiya cikin dare wanda ya saɓa wa ƙa’ida ana kallon shi ne a musabbabin wannan bala’i,” in ji shugaban Kutu Jacques Nzeza ta wayar tarho.

Ya ce mutum 29 da aka sani sun mutu sun hada da mata 15 da yaro daya.

Shugaban wata kungiyar farar hula na yankin, Fidele Lizoringo, ya ce masunta sun kara gano wasu gawarwaki hudu na shawagi a cikin kogin amma ba su iya ceto su ba.

Lizoringo ya ce an yi rajistar mutum 152 da suka tsira.

Leave a Reply