‘Yan sanda sun kama matashin da ake zargi da yin garkuwa da ‘yar maƙocinsa

0
70
'Yan sanda sun kama matashin da ake zargi da yin garkuwa da 'yar maƙocinsa

‘Yan sanda sun kama matashin da ake zargi da yin garkuwa da ‘yar maƙocinsa

Daga Shafaatu Dauda,Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama wani matashi mai suna Zakariyya Muhammad, da ake zargi da laifin yin garkuwa da ƙaramar yarinya mai shekaru biyu da rabi.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da manema labarai a ranar Talata.

Sanarwar ta ce, tun a Ranar 4 ga watan Yuli 2024, rundunar ta samu ƙorafi daga wani Mazaunin unguwar Sabuwar Gandu Kwarin Barka, cewar wani ya ƙira wayar sa inda ya shaida masa cewar ya yi garkuwa da ‘yarsa mai suna Amina , har aka nemi a biya shi kuɗin fansa naira miliyan biyu kafin ya sake ta.

Bayan samun korafin ne Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya tayar da dakarun ‘yan sanda ma su yaƙi da garkuwa da mutane, ƙarƙashin jagorancin SP Aliyu Muhammad Auwal, tare da ba Su umarnin kuɓutar da yarinyar cikin a wanni 24, da kuma kama waɗanda ake zargin.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ƙara da cewa, an yi nasarar kama wanda ake zargin Zakariya Muhammad , a ranar 5 ga watan Yuni 2024, inda ya tabbatar da cewar shi ne ya yi garkuwa da yarinyar sannan ya nemi kuɗin fansa.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Kano sun ceto ’yar shekara 2 da maƙocinsu ya sace

Neptune Prime Hausa ta kawo rahotan na cewa tuni aka kuɓutar da yarinyar kuma likitoci sun tabbatar da cewar kalau ta ke.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan Kano, ya ce an dawo da batun babban sashin binciken manyan laifuka dake Bomapai, ɓangaren da ya shafi garkuwa da mutane, kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Rundunar ta ja hankalin iyaye su dinga kula da ‘ya’yansu, tare da jan kunnen matasa cewar wannan ba abin yi ba ne, kuma ba sana’a ba ce, musamman a jihar Kano domun ma su yunƙurin aikata ba su da wajen ɓuya.