Majalisa ta amince wa Tinubu ciyo bashin $500m don sayen mitocin lantarki

0
129

Majalisa ta amince wa Tinubu ciyo bashin $500m don sayen mitocin lantarki

Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin wutar lantarki ga ’yan Najeriya.

A zaman majalisar na ranar Laraba ne ta amince wa Shugaba Bola Tinubu ya karɓo bashin daga Bankin Duniya.

Bayan karɓar rahoton kwamitin basukan ƙasashen waje ne majalisar ta amince da karɓo bashin wanda za a damƙa ga Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE).

KU KUMA KARANTA: Gwamnati ta yi wa ma’aikata da ’yan fansho ƙarin albashi

Bashin Dala miliyan 500 da za a sayi mitocin lantarkin da su wani ɓangare ne na bashin  Bankin Duniya na Dala biliyan 7.94 da Tinubu ya samu anincewar majalisar da zai karɓo a karkashin tsarin karɓar basukan kasashen waje na 2022-2024.

Da yake gabatar da rahoton, mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Haruna Manu, ya ce kudaden da mitocin za su taimaka wajen ingata samun wutar lantarki a ƙasar.

A cewarsa, aikin samar da mitocin zai ƙara ingantar karfin kamfanonin rarraba wutar lantarki da kuma samun kuɗaɗen shiga a gare su.

Leave a Reply