An ceto ɗaliban jami’ar Jihar Kogi da aka sace

Jami’an tsaro sun ceto ɗaliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi.

Rundunar haɗin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro ta ceto daliban su tara ne bayan musayar wuta da ’yan bindigar.

Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta ce a samamen da suka kaddamar a Dajin Osara, yankin da jami’ar take, suka murkushe ’yan bindigar da suka sace ɗaliban.

KU KUMA KARANTA: Muna ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban jami’ar da ‘yan bindiga suka sace – Gwamnatin Kogi

Sanarwar rundunar ta ranar Lahadi ta ce tserewa ’yan bindigar suka yi suka bar daliban, ganin cewa jami’an tsaron sun fi karkfinsu.

Rundunar ta ce sojoji sun kuma ceto wasu mutane 17 da aka sace a Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.

An ceto mutanen ne bayan daukin da sojoji suka kai inda suka bi sawun ’yan bindigar da suka sace mutanen, suka yi musayar wuta tare da ceto mutanen bayan ’yan bindigar sun tsere.

A Jihar Zamfara ma sojoji sun ceto wasu mutane biyu da aka yi sace a kauyen Danzara da ke yankin karamar hukumar Maru.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *