Kotu ta umarci ‘yansanda su biya diyyar naira miliyan 300 bisa kashe ‘yan Shi’a 3 a Zariya

0
507

Daga Idris Umar, Zariya

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta umurci hukumomin ‘yansanda da su biya zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 300 ga iyayen ‘yan Shi’a guda uku da ake zargin jami’anta sun kashe a lokacin da suke gudanar da muzahara a shekarar 2022 a Zariya.

Mai shari’a Hauwa Buhari, a cikin hukuncin da ta yanke, ta ce “’yancin masu ƙara an tabbatar da shi a cikin sashe na 33, 38, 39, 40, 42 da 46 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima); doka ta 2, da doka ta 1, 2, 3, 4 , 11 da 12 na yarjejeniyar Afrika (African Charter) kan ‘yancin ɗan’Adam da al’umma na 2004 shima an tabbatar da shi.”

Alƙalin kotun ta ce dole ne a biya adadin kuɗi har Naira miliyan 100 ga kowanne iyayen waɗanda aka kashe, inda za a biya jimillar Naira miliyan 300 ke nan a matsayin diyya da kuma ɓarnar da aka aikata, sannan za a biya ribar kashi 10 cikin 100 a duk shekara har sai an biya kuɗin baki ɗaya.

Mai shari’a Buhari, a hukuncin da ta yanke a ranar 22 ga Afrilu, 2024, inda aka bai wa manema labarai kwafin hukuncin kotun a Abuja, ta haɗa dukkanin ƙararrakin guda uku da makusantan waɗanda aka kashe guda uku suka shigar gabanta wuri guda.

“Bayan da lauyoyi suka tabbatar da ƙarar ta su tare da gabatar da shaidu, a don haka kotu ta yi la’akari da haka kuma ta ba da umurni kamar haka:

“Shari’a mai lamba: FHC/KD/CS/138/2022, da mai lamba: FHC/KD/CS/140/2022 da kuma mai lamba: FHC/KD/CS/146/2022 an hada su.

“Dole a biya kuɗi Naira miliyan 100,000,000.00 (Naira Miliyan Dari) ga kowanne iyayen waɗanda aka kashe a matsayin diyya da ɓarnar da aka yi gaba ɗaya tare da biyan ribar kashi 10% a duk shekara har sai an biya kuɗin duka.

KU KUMA KARANTA: Ka yi adalci, ka muhimmantar da ‘yancin ɗan’adam – ‘Yan Shi’a ga Tinubu

“Waɗanda aka shigar da ƙararrakin dole ne za su ba da haƙuri a rubuce ga waɗanda suka shigar da ƙara a ɗaya daga cikin jarida ta ƙasa da ke fitowa a kowacce rana saboda take haƙƙinsu da aka yi,” in ji ta.

Idan za a iya tunawa cewa mutane uku ne suka shigar da ƙarar wanda ya haɗa da; Magaji Yusuf, Muhammad Lawal da Aliyu Badamasi, inda suka shigar da ƙararrakin masu lamba: FHC / KH/ KD/ 138/2022, FHC / KH/ KD/ 140/2022 da FHC / KH/ KD/ 146/2022 a gaban kotu.

Sun yi zargin cewa a ranar 8 ga watan Agusta, 2022, jami’an ‘yan sandan Najeriya suka harbe Jafar Magaji, Aliyu Lawal da Muhsin Badamasi, a lokacin da suke gudanar da ibadarsu ta Muzaharar Ashura a garin Zariya.

Sun kai ƙarar Sufeto-Janar na ’yansanda (IGP), Mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda na shiyya ta 7, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, AC Surajo Fana (Kwamandan yankin Zariya), Ibrahim Zubairu (Jami’in ’Yansanda (DPO), Kasuwan Mata, Sabon Gari, Zaria Division), da kuma Kasim Muhammad (DPO, Zaria City Division) a matsayin masu amsa kara na 1 zuwa na 6.

Masu ƙarar a cikin ƙarar da suka shigar a ranar 26 ga Satumba, 2022 tare da kuma gabatar da ita a ranar 26 ga Satumba, 2022, ta hannun tawagar lauyoyinsu da suka hada da H.G Magashi, M.D Abubakar da Dr Yusha’u, sun nemi damarmaki guda bakwai.

Sun nemi da a bayyana cewa harbe-harbe da kashe Jafar Magaji, Aliyu Lawal da Muhsin Badamasi a ranar da aka bayyana sun gudanar da muzaharar su ta addini ya saɓawa doka, ya kuma saɓawa tsarin mulkin ƙasa, sannan ya kuma tauye haƙƙinsu na rayuwa kamar yadda sashe na 33 na kundin tsarin mulkin 1999 da kuma doka ta 4 na YarjejeniyarAfirka kan dokar hakkokin ɗan’Adam da al’umma mai lamba Cap A9 LFN na shekarar 2004 ya tabbatar.

A don haka lauyoyin suka roƙi kotun da ta umurci waɗanda ake ƙara baki ɗaya da su biya Naira miliyan 200 kowannensu saboda tauye haƙƙin ‘yan’uwansu da suka kashe.

Haka kuma sun nemi kotun ta bayar da umurni ga waɗanda suke ƙara da su rubuta takardar bayar da haƙuri tare da bugawa a cikin jaridun ƙasar nan guda biyu da ke yawo a arewacin Najeriya.

Sai dai waɗanda ake ƙara, a cikin martanin su na farko mai kwanan watan 8 ga Nuwamba, 2022 wanda suka gabatar duk a wannan kwanan wata sun nemi da kotun ta bayar da umarnin soke ƙararrakin guda ukun.

Bayan hakan kuma, sun kuma gabatar da takardar shaidar adawa da wannan ƙararrakin.

Sai dai mai shari’a Buhari ta amince da ƙara da shaidun da lauyoyin masu kara suka gabatar, inda kuma ta yanke hukunci kan hakan.

Leave a Reply