An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Ɗan’Ali a ƙaramar hukumar Ɗanmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan-ɓauna da aka kai musu.
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis kuma an ajiye gawar marigayin, mai muƙamin Manjo a wani asibiti a Katsina.
an yi wa kwamandan kwanton-ɓauna ne a ƙauyen Malali da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara, inda aka ƙira shi da ya ƙaro sojoji domin daƙile harin da aka kai ƙauyen.
KU KUMA KARANTA:Zulum ya buƙaci Sojoji su samar da sansani a dajin Sambisa
“Kamar yadda kuka sani Malali na kan titin Zangon Pawwa, kuma yankin gaba ɗaya ‘yan bindiga sun ƙwace. A duk lokacin da aka kai hari jami’an tsaro sukan nemi a kawo musu ɗauki daga sansanin Maraban Ɗan’Ali, kuma wannan sabon kwamandan zai mayar da martani cikin gaggawa.
“A wannan karon sun nemi a ƙara masa jami’an soji, ya zo ne da wata mota ƙirar Hilux, maimakon tankar yaƙi, wataƙil tamkar ba ta samu ba a lokacin. Abin takaicin shi ne kawai sai maharan da suka kai masa hari, sun harbi motar sannan shima su ka harbe shi a ka.”
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa, a yayin da ake ƙoƙarin ɗauko gawarsa daga wurin da lamarin ya faru, an yi artabu da muggan makamai tsakanin ‘yan bindigar da jami’an soji, inda jami’in da ya ɗauko gawar shi ma ya samu rauni na harbin bindiga.