Ba ƙarancin takardun kuɗi ba ne a ƙasar, yawan tsabar kuɗin dake hannun jama’a muke so a rage – CBN

0
96

A daidai lokacin da wasu ‘yan Najeriya ke ƙorafe-ƙorafe a kan ƙayyade yawan kuɗin da za su riƙa cira a ATM ko kuma a cikin banki da ake kallo a matsayin yiwuwa akwai ƙarancin takardun kuɗi ne a ƙasar, masu ruwa da tsaki a fannin hada-hadar kuɗi a bankuna sun ce babu matsalar ƙarancin kuɗi.

Sun ce illa dai ana ƙoƙarin ƙarfafa wa ‘yan ƙasa da su riƙa amfani da hanyoyin yanar gizo wato electronic channels wajen samun biyan buƙata ne don rage yawan tsabar kuɗin dake zirga-zirga a cikin ƙasar.

Babban Bankin Najeriya CBN dai ya ce kuɗaɗen da ke zirga-zirga a ƙasar sun kai Naira tiriliyan uku da biliyan 690 a watan Fabrairun da ya gabata wanda shi ne adadi dake zirga-zirga mafi yawa a tarihin ƙasar.

Alƙaluman da suka bayyana haka bayan taron kwamitin manufofin kuɗin bankin wato MPC wanda aka sanar a ranar talata 26 ga watan Maris da muke ciki.

‘Yan Najeriya daga sassa daban daban sun yi ta ƙorafi dai a kan taƙaita adadin kuɗin da za su iya cira a cikin banki ko a ATM kamar yadda wani ɗan ƙasa, Abdulaziz Mala ya ce ya je cire kuɗi kuma dubu 5 kawai ya iya cira.

Saidai wani jigo a bankin Access ya shaida wa Muryar Amurka ta wayar tarho cewa taƙaita iya kuɗin da mai asusu zai iya cira abu ne na bai ɗaya a dukkan bankuna ne kuma wani sashi ba zai iya ƙayyade yawan kuɗin da za’a iya cira ya bambanta da na sauran ba.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta umurci CBN ta biya wani Bajamushe naira Miliyan 63 da ta tsare ba bisa ƙa’ida ba

Yana mai cewa mutum zai iya cire Naira dubu 20 sau huɗu a machine ɗaya kuma matakin rage tsabar kuɗin da za’a iya cira ba ya rasa nasaba da ƙoƙarin rage yawan kuɗin dake zirga-zirga a cikin ƙasa wanda ya samo asali tun lokacin sauya launin kuɗi.

A wani ɓangare kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum Suleiman Hashim ya bayyana cewa bankin CBN ƙarƙashin Gwamna Olayemi Cardoso ya ɗora a kan dokar nan na rage yawan tsabar kuɗi dake cikin ƙasar ne saboda adadin dake yawo shi ne mafi girma a tarihin ƙasar.

Alƙaluman kididdiga na baya-bayan nan dai sun yi nuni da cewa an sami ƙari a adadin Naira dake zirga-zirga a cikin ƙasar da kaso 1.8 cikin 100 na wata-wata daga Naira tiriliyan 3.65 da aka sanar a watan Janairun shekarar 2024 da muke ciki.

Idan ana iya tunawa tun bayan batun sauya launin kuɗi ake fama da matsalar adadin yawan kuɗi da mutane za su iya cira a cikin asusunsu na banki lamarin da wasu ‘yan kasuwa ke ƙorafe-ƙorafe a kan wanda har yanzu akwai mutane masu ɗimbim yawa da ba sa amfani da hanyoyin yanar gizo wato electronic channels wajen hada-hadar kuɗinsu na yau da kullum.

Leave a Reply