Boko Haram ta saki mata tara daga cikin sama da mutum 200 da ta sace a Najeriya  

Boko Haram ta saki aƙalla ƴan gudun hijira tara daga cikin sama da 200 da ƙungiyar ta yi garkuwa da su a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, a cewar jami’ai a ranar Litinin.

Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA, Barkindo Saidu ya ce an ga mutanen tara, waɗanda duka mata ne da ƴan mata, a sansanin ƴan gudun hijira na Ngala a jihar Bornon da ke arewa maso gabashin ƙasar.

“Ma’aikatan sansanin ƴan gudun hijirar sun ba da rahoton cewa mutum tara sun koma. An gan su a sansanin ƴan gudun hijirar,” kamar yadda Saidu ya shaida wa Anadolu ranar Litinin.

Sama da mata 200 da ƴan mata da maza, wadanda suka bar sansanin gudun hijirarsu don neman itace a Ngala da ke yankin arewa maso gabashin jihar Borno mayaƙan Boko Haram suka yi garkuwa da su.

Ƙungiyar yan ta’addan wacce ke da matsuguninta a yankin arewa maso gabashin Najeriya kana ta yi karfi a Chadi da Nijar da arewacin Kamaru da kuma Mali.

A ƴan shekarun nan, matsalar masu garkuwa da mutane da kuma yan fashi sun ɗaɗa ƙaruwa sosai a ƙasar da ke yankin Yammacin Afirka.

KU KUMA KARANTA: Mayaƙan Boko Haram sun sace mata 319 a Borno

Kimanin muyum 430 galibi mata da yara ne aka yi garkuwa da su a yankin arewacin ƙasar cikin ƴan makonni biyu da suka wuce.

Abubakar Boyi Sifawa, babban mai bincike a kan dabi’u da tsaro a Jami’ar Ilimi ta Shehu Shagari da ke arewa maso yammacin jihar Sakkwato, ya ɗora alhakin yawan sace-sacen jama’a da ƴan fashi da makami ke yi a kasar kan taɓarɓarewar tattalin arziki da talauci da rashin haɗin kai a tsakanin hukumomin tsaro.

“A bisa binciken da na yi, abin takaici, matasa da yawa a yanzu suna shiga ƙungiyoyin satar mutane da kuma masu ba da labari don a biya su saboda matsalar tattalin arziki, suna gaggawar su samu kuɗi saboda talauci, sannan suna fada wa cikin kungiyoyin ta’addanci bayan sun karɓa kuɗin fansa,” kamar yadda Boyi Sifawa ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Turkiyya Anadolu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *