‘Yansandan a jihar Neja sun kama matan da ake zargin sun shirya zanga-zangar tsadar rayuwa

Daga Maryam Umar Abdullahi

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta ce ta kama wasu mata guda uku da ake zargin suna da hannu wajen shirya zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a jihar Neja a ranar Litinin ɗin nan da ta gabata.

Wata sanarwa daga Kakakin ‘yansandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ta nuna sun kama wata Aisha Jibrin mai shekaru 30 da suka ce ita ce ta tsara yadda aka gudanar da wannan zanga-zangar.

Sauran matan sun haɗa da Fatima Aliyu ‘yar shekaru 57, da kuma Fatima Isyaku mai shekaru 43. Ko baya ga wannan dai ‘yansandan sun ce sun kama wasu matasa 24 da suke zargin suna da hannu wajan shiga wannan zanga-zanga.

Dama dai tuni gwamnatin jihar Nejan ta ce masu zanga-zangar ta ranar Litinin sun yi ne domin satar kayan wata babbar mota kamar yadda gwamnan jihar, Umar Bago ya bayyana mana.

KU KUMA KARANTA:Najeriya ta ƙaddmar da Jirage biyu don yaƙi da masu tada ƙayar baya

To sai dai masu sharhin akan lamura sun yi Allah wadai da kama waɗannan mata.

Itama dai ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam a jihar Neja ta bayyana rashin jin daɗinta akan kama waɗannan mutane kamar yadda Shugaban ƙungiyar na jihar Neja Kwamred Abubakar Abdullahi ya shaida mana.

Rudunar ‘yansandan dai ta ce da zarar ta kammala bincike akan mutanen za ta gurfanar da su ne gaban kotu domin fuskantar hukunci.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *