Najeriya ta ƙaddmar da Jirage biyu don yaƙi da masu tada ƙayar baya

0
218

Daga Maryam Umar Abdullahi

A cewar mataimakin Shugaban Najeriyar ƙaddamar da jiragen na cikin ƙudurorin gwamnatin tarayya na yaƙar matsalar tsaron da ke addabar ƙasar.

Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyar magance matsalar tsaron da ke addabar sassan Najeriya ta hanyar ƙarfafa rundunonin yaƙi da masu tada ƙayar baya.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar da jirgi mai sauƙar ungulu samfurin “ti29 atak combat helicopter da kuma wani samfurin “beecraft king air 360er”, a sansanin sojin sama a Makurɗi, babban birnin jihar Binuwe tare da wani jirgin dakon kaya da zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan rundunar ta sama a ƙoƙarin ta na fatattakar ‘yan ta’adda.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya samu jinjina daga jama’a a yayin da yake ƙaddamar da jirgin yaƙi samfurin “T129 atak helicopter”, inda aka gudanar da atisayen gwajin yadda yake aiki da kuma sauƙin sarrafarwarsa a cikin iska.

KU KUMA KARANTA:Ƙungiyar ƙwadago ta yi watsi da ƙarin dubu 10 da gwamnan Jigawa ya yi wa ma’aikata

Ɗaya daga cikin sabbin jiragen da Kashim Shettima ya ƙaddamar
ɗaya daga cikin sabbin jiragen da Kashim Shettima ya ƙaddamar
Gwamnan Jihar Binuwe, Hyacinth Alia, ya yabawa gwamnatin tarayya tare da bayyana fatan samun ƙarin ƙaimi a yaƙin da take yi da muggan laifuffuka da ta’addanci.

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas, ne ya jagoranci mambobin majalisar wajen bikin ƙaddamar da jiragen a wani mataki na nuna goyon baya.

Leave a Reply