INEC ta dakatar da wani jami’inta don gudanar da bincike kan ɓacewar takardun kaɗa ƙuri’a

Daga Maryam Umar Abdullahi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta dakatar da wani jami’inta mai suna Mr Fred Ogboji, wanda ke kula da ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, bisa zargin ɓacewar wasu muhimman kayayyakin gudanar da zabe.

Hukumar INEC, a wata sanarwa ta ce ta dakatar da jami’in nata ne don samun sukunin gudanar da bincike a kan ɓacewar takardun kaɗa ƙuri’a na kujerar majalisar wakilai na shiyyar Bassa da Jos ta Arewa a rumfuna goma sha shida, a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Jami’a a sashen yaɗa labarai na hukumar INEC, Zainab Aminu, ta tabbatar da dakatar da jami’in, don yin bincike.

Duk da umurnin sake yin zaɓen a ranar Lahadi a wasu rumfuna, jami’an zaɓe ba su fito a kan lokaci ba, yayin da a wasu rumfunan jama’a ba su fito don sake gudanar da zaɓen ba.

KU KUMA KARANTA:Ministan Wajen Turkiyya ya yi gargaɗi  kan yiwuwar ɓarkewar rikici, saboda harin da Amurka ke kai wa ƙungiyoyin da Iran ke goyon baya

Mr. Raphael Madugu, wani ɗan jarida a jihar Filato, ya ce sun yi ta ƙoƙarin samun jami’in hukumar zaɓen don ya yi bayani kan matsalolin da aka fuskanta a rumfunan zaɓen amma bai amsa ƙira da saƙonni da aka aike masa ba.

An gudanar da zaɓen Sanata na shiyyar Arewacin jihar Filato da na majalisar wakilai na Jos ta Arewa da Bassa ne bayan da kotu ta soke waɗanda aka zaɓa a ƙarƙashin jami’iyyar PDP, bayan da ta ce jami’iyyar ba ta da zaɓaɓɓun shugabanni a jihar Filato a lokacin da aka gudanar da zaɓukan gama gari a shekara ta dubu biyu da ashirin da uku.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *