An ceto manoma 16 daga hannun masu garkuwa da mutane a Neja

Daga Maryam Umar Abdullahi

An buɗe makarantun firamare da ke rufe tsawon shekaru a yankin saboda dalilai na matsalar tsaro.

Manoma 16 sun shaƙi iskar ’yanci bayan jami’an tsaro sun ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane a ƙauyen Ɗan Gunu da ke ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja.

Shugaban ƙaramar hukumar Munya, Abdulhamid Najume ne ya bayyana hakan yayin zantawa da wakilinmu ta wayar tarho a ranar Asabar.

Rahotanni sun ruwaito cewa, a Larabar makon jiya ce ’yan bindiga suka kai hari ƙauyen na Ɗan Gunu, inda suka yi awon gaba da waɗanda abin ya shafa ciki har da mata masu juna biyu da ƙananan yara.

A cewar Shugaban Ƙaramar Hukumar, an samu nasarar ceto manoman ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro da aka gudanar.

Ya bayyana cewa hakan ce ta sanya aka bazama tare da bin sahun ’yan ta’addan, lamarin da ya kai ga ceto mutanen.

KU KUMA KARANTA:An haifi yara ‘yan biyu maza a haɗe a Sakkwato

Ya ƙara ceto, mutanen da aka ceto na ci gaba da samun kulawa a asibiti domin tabbatar da lafiyarsu kuma daga bisani za su koma cikin ’yan uwansu.

Dangane da makarantun firamare da ke rufe tsawon shekaru a yankin saboda dalilai na matsalar tsaro, Najume ya ce an buɗe makarantun inda ɗalibai za su ci gaba da karatunsu.

Kazalika, ya ce an yi gyare-gyare a wasu daga cikin makarantun da aka buɗe domin ci gaba da harkokin karatu ba tare da wata tangarɗa ba.

“Mun rarraba kayayyaki kamar alli da littafan rubuta da sauran kayayyakin karatu musamman domin tallafa wa iyayen ɗaliban da ba su da halin ɗaukan wannan nauyi.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *