Daga Ibraheem El-Tafseer
Hukumomin yankin Valparaíso na ƙasar Chile sun ce aƙalla mutane 51 ne suka mutu sakamakon gobarar dajin da ta tashi a yankin.
Shugaban ƙasar, Gabriel Boric ya ayyana dokar ta-ɓaci, sannan ya ce zai yi “duk abin da ya dace” don magance matsalar.
An yi amanna cewa wannan ce gobarar daji mafi muni a tarihin Chile.
Yawancin waɗanda gobarar ta shafa na ziyara ne a yankin wanda ke a gaɓar teku domin hutun lokacin bazara.
Ma’aikatar lafiyar ta yi ƙiran dakatar da tiyatar da ba ta zama dole ba a asibitocin wucin-gadin da za a kafa.
KU KUMA KARANTA: Gobara a cibiyar sayar da gas a Kenya, ta kashe mutum 2 da jikkata fiye da 300
Za a ɗauki daliban likitancin da ke dab da kammala karatunsu domin taimaka wa likitoci wajen rage musu wahalhalun aiki, kamar yadda ma’aikatar lafiyar ƙasar ta bayyana.
Jami’an ceto na kokawar isa yankunan da lamarin ya fi ƙamari.
Ministar harkokin cikin gida ta ƙasar, Carolina Tohá ta ce adadin waɗanda suka mutu ”zai iya ƙaruwa“, nan da sa’o’i masu zuwa.
Gwamnatin ƙasar na shawartar mutane da su guji zuwa wuraren da gobarar ta shafa.