Yau ce ranar zaɓen cike gurbi da raba gardama a jihohi 26 na Najeriya

Daga Maryam Umar Abdullahi

An hana zirga-zirgar ababen hawa har zuwa shida na yamma a jihohin da za a yi zaɓen.

A yau Asabar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke gudanar da zaɓukan raba-gardama da kuma na cike giɓi na kujerun majalisun tarayya da kuma na jihohi a 26 a ƙasar.

Za a gudanar da zaɓukan ne a ƙananan hukumomi 80 a faɗin Najeriya, domin cike gurbin wasu da suka rasu da ’yan majalisar da kotu ta cire ko kuma waɗanda suka sauka domin karɓar wasu muƙaman.

A cewar Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, za a yi zaɓen cike gurbi ne a jihohi tara daga cikin 26 domin zaɓar sanatoci biyu da ’yan majalisar wakilai na tarayya huɗu da kuma kujeru uku na majalisar jiha.

A zaɓukan gaba-ɗaya za a yi na kujerun sanatoci uku da kujerun majalisar wakilai 17 da kujeru 28 na majalisun jihohi a faɗin ƙananan hukumomi 80.

Wasu daga cikin fitattun kujerun da za a yi zaɓen nasu su ne, kujerar Honarabul Femi Gbajabiamila, wanda ya yi murabus ya karɓi mukamin Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban ƙasa, da ta Sanata David da Sanata Ibrahim Geidam da Honarabul Bumi Tunji-ojo da Honarabul Tanko Sununu da suka yi murabus domin karɓar muƙamin ministoci.

Akwai kuma kujerar majalisar wakilai ta Honarabul Isma’ila Maihanchi, daga Taraba, wanda ya rasu tun kafin rantsar da shi da kuma Honarabul Abdulƙadir Danbuga daga Sokoto wanda ya rasu a watan Oktoba na 2023.

KU KUMA KARANTA:Babban jami’in MƊD ya damu da yiwuwar kai farmakin da Isra’ila ke yi a Rafah

Jihohin da za a yi zaɓukan sun haɗa da Ebonyi, da Yobe, da Kebbi, da Legas, da Ondo, da Taraba, da Benuwe, da Borno, da Kaduna, da Filato, da Akwa Ibom, da Anambara, da Kuros Riba, da Delta, da Enugu, da Jigawa, da Katsina, da Adamawa, da Bauchi, da Bayelsa, da Kano, da Nasarawa, da Neja, da Oyo, da Sokoto, da kuma Zamfara.

Dangane da zaɓukan Babban Sufeton ‘Yan-sanda Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin hana zirga-zirgar ababen hawa daga ƙarfe 12 na dare zuwa shida na yamma a jihohin da za a yi zaɓen.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da al’umma na rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyi Adejobi ya fitar tun a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce dokar taƙaita zirga-zirgar ba ta shafi masu muhimman ayyuka ba, kamar ma’aikatan kashe gobara da ‘yan jarida da jami’an INEC da likitoci da masu sanya ido a zaɓukan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *