Kotu ta bayar da umarnin kama Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi

0
161

Kotun Shari’ar Musulunci a jihar Bauchi da ke Najeriya, ta mayar wa da waɗanda suka tsaya wa Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi takardun ƙadarorinsu da suka bayar domin karɓar belin shi da ta bayar a baya.

Wannan mataki dai na nufin kotun ta janye belin da ta bayar kan Dakta Idris, wanda kuma hakan yake nufi a kowanne lokaci za a iya kama shi.

Barista Ahmad Musa Umar shi ne lauyan da ke kare Dr Idris, ya ce “kotu za ta iya bai wa ‘yan sanda takardar kama Dakta Idris a kowanne lokaci”.

“Kotun ta ce ta ɗage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan nan na Janairu, wanda kuma take tsammanin jami’an tsaro sukai mata shi gabanin wannan rana,” in ji Barista Ahmad Musa.

Ana dai tuhumar Dakta Idris ne da laifuka biyu, na farko kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ba da belin Dakta Idris Dutsen Tanshi bisa sharaɗi

Na biyu kuma ana tuhumarsa da laifin tayar da zaune tsaye.

Har yanzu dai ba a fara sauraran wannan shari’a ba kan waɗannan tuhume-tuhume.

Amma a baya ya yi zaman gidan kaso kan waɗannan tuhume-tuhume na tsawon kwana 39 tsakanin watan Yuni da Yuli, in ji lauyansa.

Leave a Reply