Majalisar Amurka ta yi watsi da ƙudirin janye dakarun ƙasar daga Nijar

0
159

A halin yanzu akwai kimanin dakarun Amurka 1,000 da ke aikin kakkaɓe ’yan ta’adda a ƙasar ta Jamhuriyar Nijar.

Majalisar Dattawan Amurka ta yi fatali da wani ƙuduri da zai buƙaci Shugaba Joe Biden ya janye dakarunsu daga Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.

A ƙuri’ar da suka kaɗa a kan ƙudurin, ’yan majalisa 86 sun yi watsi da shi yayin da 11 suka amince da shi.

A watan nan ne Amurka ta bayyana a hukumance cewa an yi juyin mulki a Nijar, abin da ya sa ta daina bai wa ƙasar tallafi kamar yadda dokarta ta ce.

Sai dai wasu daga jami’an gwamnati sun ce ba a buƙatar janye dakarun ƙasar daga Jamhuriyar Nijar.

Amurka ta daɗe da ƙulla yarjejeniyar tsaro da Nijar inda suke yaƙi da ’yan ta’adda da ke da alaƙa da ƙungiyar Al Qaeda da ISIS a yankin Sahel.

KU KUMA KARANTA: Amurka ta soke tallafin dala miliyan 442 da take ba wa Nijar

A halin yanzu akwai kimanin dakarun Amurka 1,000 da ke aikin kakkaɓe ’yan ta’adda a ƙasar ta Jamhuriyar Nijar.

Sanata na jam’iyyar Republican, Rand Paul, wanda ya ɗauka nauyin ƙudurin, ya dage cewa ba a bi ƙa’ida ba wajen aika sojojinsu Jamhuriyar Nijar.

A cewarsa, majalisar dokoki ba ta amince da matakin ba tun da farko abin da ke jefa dakarun ƙasar cikin hatsari.

“Tun da yanzu ana rikici a Gabas ta Tsakiya, wacce hujja muke da ita ta barin dakaru fiye da 1,000 a Nijar?

“Shin akwai hikima a bar dakaru sama da 1,000 a ƙasar da sojoji suka yi juyin mulki?” kamar yadda Sanata Paul ya bayyana a jawabin da ya gabatar a zauren majalisar dattawan.

Sai dai Sanata Ben Cardin na jam’iyyar Democrat kuma shugaban kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar, ya ce za a samu gagarumin giɓi a yankin Sahel idan aka janye dakarun ƙasar daga Nijar.

Ya bayyana cewa janye dakarun zai bai wa Rasha da ƙungiyar sojojin haya ta Wagner damar cin karensu babu babbaka a yankin.

“Ba ma mayar da hankali sosai a wannan yankin na duniya. Don haka bai kamata mu nuna alamun cewa mun yi watsi da lamuran yankin ba,” in ji Cardin.

Tuni dai Faransa, wadda ta yi wa Nijar mulkin-mallaka, ta soma janye dakarunta fiye da 1,500 daga Jamhuriyar Nijar bayan dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa Mohamed Bazoum.

Leave a Reply