Matsalar garkuwa da mutane na daga cikin matsalolin tsaro a Kamaru.
A ƙalla mutane 30 ne ake fargabar an yi garkuwa da su, ciki har da ɗalibai a Arewacin Kamaru.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa mutanen da aka sace sun fito ne daga ƙasar Chadi mai maƙwaftaka kamar yadda Magajin Garin Touboro ya bayyana a ranar Litinin.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da daddare, kamar yadda Magajin Gari Celestin Yandal ya ce.
Wata majiya daga ɓangaren tsaron Kamaru ta tabbatar da faruwar lamarin ba tare da bayar da bayanai kan yadda lamarin ya faru ba, inda ta ce tana zargi an yi garkuwa da su ne domin karɓar kuɗin fansa wanda ba sabon abu ba ne a yankin.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari kan bankuna a Benuwe, sun kashe mutane takwas
Majiyar ta ce ba a tabbatar da ko su wane ne waɗanda aka sace ba amma mai yiwuwa akwai ɗalibai ‘yan Chadi daga cikinsu.
Ɗalibai daga Chadi na bin hanyar Touboro domin zuwa birnin Ngaoundere don yin karatun jami’a.
Kamaru na fuskantar matsaloli da dama na tsaro waɗanda suka haɗa da na Boko Haram a Arewa mai nisa da kuma rikicin ‘yan a-ware a yankin renon Ingilishi.