‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama, sun yi garkuwa da wasu a Kano

0
198

Ana fargabar cewa wasu ’yan bindiga sun kwashe wani adadi na jama’ar ƙauyen Yola da ke ƙaramar Hukumar Ƙaraye a Jihar Kano.

Lamarin na zuwa ne bayan wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan daban daji sun kai hare-hare a yankuna daban-daban na ƙauyen.

Bayanai sun ce hare-haren da aka kai yankuna daban-daban sun yi sanadiyyar mutuwar jama’a da dama yayin da aka yi garkuwa da wasu.

A cewar wani mazaunin ƙauyen da ya buƙaci a sakaya sunansa, hare-haren sun auku a yankuna daban-daban na ƙauyen da ba zai iya fayyace adadin mutanen da aka kashe ko aka yi garkuwa da su ba.

“Na samu labarin cewa a rana ta farko sun sace mutum Huɗu sannan sun kashe wasu mutum biyu.

“Haka kuma a rana ta biyu sun kashe ƙarin wasu mutum biyu tare da garkuwa da mutum ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe basarake sun ƙona gawarsa a Imo

“Sai dai ba ni da tabbaci kan alƙaluman mutanen da aka sace ko aka kashe.

“Amma ba na tantamar cewa an ɗauke wasu mutane kuma an kashe wasu.

“Abin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne Ƙaraye tana buƙatar dakarun soji su kawo mana ɗauki saboda waɗannan hare-hare,” a cewarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa, a bayan nan yankunan ƙaramar Hukumar Ƙaraye da Rogo na fuskantar matsalolin tsaro saboda kusancinsu da Jihohin Kaduna da Katsina.

Ana iya tuna cewa, a watan Afrilun da ya gabata ne wasu ’yan daban daji suka kashe wani mutum ɗaya tare yin garkuwa da wani ɗan kasuwa a ƙauyen Gangarbi da ke ƙaramar Hukumar Rogo, Alhaji Nasiru Na’ayya.

Kazalika, a shekarar 2021 ce Masarautar ƙaraye ta yi koken yadda ake samun kwararowar masu haƙar ma’adanai daga Jihar Zamfara.

Wasu majiyoyi sun ce tuni masarautar ta ɗauki matakam da suka dace domin yi wa tufkar hanci.

Sai dai ƙoƙarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin mai magana da yawun da rundunar ’yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura a yayin da bai amsa ƙiran wayarsa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Leave a Reply