Dalilan da ya sa maganin tazarar haihuwa ke haifar da illoli ga mata

0
327

Daga Ibraheem El-Tafseer

A wannan rubutu da Aisha Salisu Babangida ta yi, a kan wannan matsala ta fara ne da cewa; Magungunan hana ɗaukar ciki sun zama muhimmin al’amari ga ma’aurata, musamman ma mata da ke amfani da su wajen ba da tazarar haihuwa da tsara rayuwar iyali.

Irin waɗannan magunguna, sun ƙunshi hanyoyi daban-daban, kama daga magungunan sha zuwa allurai da robar da ake sanya wa mata a dantsensu, da dai sauransu.

Da yawan mata na ganin fa’idar amfani da magungunan hana ɗaukar ciki, amma wasu sun ce sukan fuskanci matsaloli da dama da ke zuwa bayan amfani da su.

Waɗansu matsalolin da mata ke fuskanta sakamakon amfani da magungunan hana ɗaukar ciki kamar yadda Maryam da Faiza, wasu iyaye mata masu amfani da irin waɗannan magunguna suka shaida wa BBC, su ne; matsalolin al’ada da ƙarin ƙiba da amai.

KU KUMA KARANTA: Abincin Najeriya da masu neman haihuwa ya kamata su ci

Akwai ma ciwon Nono da ciwon kai da rage sha’awar jima’i da fitowar wani ruwa daga al’aura da dai sauransu.

Waɗannan matsaloli suna kuma haifar da rashin jituwa a tsakanin ma’aurata in ji su.

Leave a Reply